1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel za ta kebe kanta saboda fargabar Corona

March 22, 2020

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta kebe kanta daga jama'a a saboda fargabar kamuwa da cutar Coronavirus.

Deutschland Merkel muss wegen Kontakt zu Corona-Infiziertem in Quarantäne
Hoto: AFP/M. Kappeler

Wannan ya biyo bayan duba lafiyarta da wani likita wanda rahotanni suka ce yana dauke da cutar Corona yayi. Mai magana da yawun shugabar, Steffen Seibert, ne ya sanar da haka a wannan Lahadi.

A cikin sanarwar da Seibert ya fitar ya ce likitan ya duba lafiyar Angela Merkel a juma'ar da ta gabata da niyyar ya yi mata rigafin wata cuta na'u'in Bacteria. Amma kuma a yau din nan aka sanar da ita cewa wannan likita yana dauke da Corona. Sai dai Seibert ya ce za a dan dauki lokaci mai tsawo kafin a iya tantance ko Merkel ta kamu da cutar ko kuma a'a.

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: AFP/M. Kappeler

 

Mai magana da yawun Merkel din ya ce duk da cewa za ta keba kanta amma harkokin gwamnati za su ci gaba kamar yadda aka saba, inda za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta daga gida.

A cikin shekaru 15 da Angela Merkel ta kwashe tana jagorantar Jamus shugabar ta kasance cikin koshin lafiya. Sai dai an taba ganin jikinta yayi kyarma a bayyanar jama'a.

Wannan labari mara dadi ga mazauna Jamus dai na zuwa ne 'yan awanni bayan Angela Merkel ta gudanar da taro da Shugaban Kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da shugabannin jihohi 16 na kasar a kan yadda za a magance cutar Coronavirus a kasar, inda har ma ta sanar da cewa ta haramta duk wani taro da ya wuce na mutum biyu a kasar.