1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Turkiyya ya kawar da yuwuwar jinkirta zabe

Suleiman Babayo ZAM
March 1, 2023

Shugaban kasar Turkiyya ya kawar da yuwuwar jinkirta zaben shugaban kasa samakon girgizar kasa da aka samu

Turkiyya | Shugaba Recep Tayyip Erdogan a birnin Ankara
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na TurkiyyaHoto: Depo Photos/ABACA/picture alliance

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya a wannan Laraba ya kawar da yuwuwar jinkirta zaben shugaban kasa da aka tsara ranar 14 ga watan Mayu saboda girgizar kasa da aka samu a cikin watan Febrairun da ya gabata.

Yayin jawabi ga 'yan majalisar dokoki na bangaren jam'iyya mai mulki a birnin Ankara fadar gwamnatin kasar, shugaban ya ce mutanen Turkiyya za su yi abin da ya dace ranar 14 ga watan Mayu mai zuwa.

Bayan samun girgizar kasa a kasashen Turkiyya da Siriya an zaci gwamnatin za ta jinkirta zaben na watan Mayu ganin kimanin mutane dubu-45 iftila'in ya halaka a kasar ta Turkiyya, kuma lokacin Shugaba Erdogan ya kafa dokar ta-baci ta watanni uku a yankuna 11 na kasar da aka samu girgizar kasar.