1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Za a yi zaben sabon shugaban Koriya ta Kudu ranar Talata

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 2, 2025

A ranar Laraba hukumar zaben Koriya ta Kudu za ta bayyana kammalallen sakamakon zaben bayan tattara kuri'un da aka jefa.

Jerin masu yin zabe a Koriya ta Kudu
Hoto: Ahn Young-joon/AP Photo

Ranar Talata al'ummar kasar Koriya ta Kudu za su kada kuri'ar zabar sabon shugaban kasa, wanda zai kawo karshen dambarwar siyasar da aka shafe watanni ana gwabzawa, wadda ta yi awon gaba da kujerar dakataccen shugaba Yoon Suk Yeol.

Za a bude rumfunar zabe da karfe 6 na safiya agogon kasar zuwa 8 na dare, wanda ake sa ran fitar farin dango na miliyoyin mutanen kasar don dangwala kuri'a.

karin bayani:Lee Ju Ho ya zama mukaddashin shugaban Koriya ta Kudu

A ranar Laraba hukumar zaben Koriya ta Kudu za ta bayyana kammalallen sakamakon zaben bayan tattara kuri'un da aka jefa.