Za a zabi sabon shugaban kasa a Somaliya
June 29, 2021Talla
Firaministan na Somaliya Mohamed Hussein Roble ya shaida wa kamfanin dillancin labaran kasar na SONNA cewa, biyo bayan wata doguwar tattauna wa tsakanin kwamitin dattawan kasar da jam'iya mai mulki, dattawan zasu zabi 'yan majalisar da zasu zabi sabon shugaban a ranar 10 ga watan Oktoba mai zuwa.
Tun da fari dai hukumar zaben kasar ta bayyana cewa ba za ta iya gudanar da zabe ba sakamakon kalubalen tsaro da ake fama da shi, wanda ya baiwa kwamitin dattawa damar zaben masu zaben shugaba a Somaliya shekaru da dama da suka gabata.