1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za mu ci-gaba da gwajin makamai: Jong Un

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
December 28, 2022

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya sanar da sabbin manufofin kasar ta fannin tsaro da tattalin arziki da diflomasiyya na sabuwar shekara a babban taron jam'iyyar da ke mulki.

Nordkorea Raketentest Kim Jong Un
Hoto: KCNA via REUTERS

Kamfanin dillancin labaran Koriya ta Arewa KCNA ya fada a ranar Laraba cewa Kim Jong Un ya fayyace sabbin manufofin soji don karfafa abin da ya kira ikon kare kai, wanda za a aiwatar da shi a shekara ta 2023.

A halin yanzu dai shugaban na Koriya ta Arewa na jagorantar wani babban taron shekara-shekara na daya-dayar jam'iyyar kasar a Pyongyang babban birnin kasar, inda shi da wasu manyan shugabannin jam'iyyar suka bayyana manufofinsu na siyasa a shekarar 2023 game da muhimman fannoni kamar diflomasiyya da tsaro da tattalin arziki. Dama dai taron na karshen shekara a Koriya ta Arewa na baiwa gwamnatin damar bayyana abubuwan da kasar ta sa gaba a ciki da wajenta.

Koriya ta Arewa mai amfani da makamin Nukiliya ta gudanar da gwaje-gwajen makaman da ba a taba ganin irinsa ba a bana, ciki har da harba makami mai linzami da ake kira ICBM, inda ta ci gaba da bijirewa takunkumin Majalisar Dinkin Duniya. 

A ranar Litinin din da ta gabata ma dai, sojojin Koriya ta Kudu sun kuma sanar da cewa, sun jibge jiragen yaki da jirage masu saukar ungulu bayan kutsa kai cikin yankinsu na jiragen yakin Koriya ta Arewa guda biyar, daya daga cikinsu ya isa sararin samaniyar birnin Seoul.