Za'a ƙafa gwamnatin ƙawance a Isra'ila
May 8, 2012Da safiyar talartar nan ce firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da jagorar adawar ƙasar Shaul Mofaz suka amince da ƙafa gwamnatin haɗin kan ƙasa. Wannan yarjejeniyar dai na da nufin kaucewar yiwuwar gudanar da zaɓuka cikin watan Satumba, inda a yanzu za'a gudanar da zaɓen ne kamar yanda aka tsara tunda farko, wato cikin watan Oktoban shekara ta 2013. A ƙarƙashin wannan yarjejeniyar da aka cimma da jagorar jam'iyyar Kadima Shaul Mofaz daya ɗare muƙamin shugabancin jam'iyyar kimanin makonni shiddan da suka gabata dai, shi ne zai kasance muƙaddashin firaminista kana da muƙamin ministan amma wanda ba shi da wata ma'aikata a cikin majalisar ministocin ƙasar.
Ko da shike sai nan gaba ne sassan biyu za su fayyace abubuwan dake cikin yarjejeniyar, amma jam'iyyar Kadima za ta goyi bayan Netanyahu a ƙoƙarin daya ke yi na samar da sauye sauye ga tsarin mulkin ƙasar, yayin da wasu mambobin jam'iyyar Kadimar kuwa za su sami muƙamai a cikin kwamitocin majalisar dokokin Isra'ila dake kula da harkokin tsaro, da na tattalin arziƙi da kuma na harkokin waje. Mofaz dai tsohon hafsan soji ne kuma ministan tsaro.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : zainab Mohammed Abubakar