Indiya: Za a sake bude makarantu a Kashmir
August 16, 2019Talla
Babban mai shari'ar kasar ta Indiya shi ne ya sanar da hakan a wannan Juma'ar, bayan da kotun kolin ta saurari karar kalubalantar matakin na gwamnati.
Wani jami'i a lardin na Kashmir ya sanarwa da manema labaru cewar nan ba da jimawa ba, za'a fara bude layukan tarho na gidaje da aka toshe, a yayin da makarantu zasu bude a ranar Litinin mai zuwa.
Sai dai bai fadi lokacin da za a bude layukan wayoyin hannu ba, wadda a cewar gwamnati 'yan ta'adda na iya amfani dasu.
Tun bayan da gwamnati ta sanar da soke 'yancin kan Kashmir din da mafi yawan al'ummarta musulmi ne, yankin ya cigaba da kasancewa cikin wani yanayi mai kama da dokar-hana-fita, daura da jami'an tsaro da ke cigaba da sintiri.