1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za'a yi garon bawul a gwamnatin Masar

Zainab MohammedApril 29, 2012

Shugaban majalisar mulkin soji Hussein Tantawi ya sanar da wannan tankaɗe da rairaya gabanin zaɓen shugaban ƙasa, karon farko bayan hamɓarar da Mubarak.

Field Marshal Mohamed Hussein Tantawi, head of Egypt's ruling military council, points to a painting as he accompanies Turkish Prime Minister Recep Tayyip Erdogan, not pictured, at the defence ministry in Cairo, Egypt, Tuesday, Sept. 13, 2011. Erdogan, intent on broadening Turkey's influence in the Middle East and the Arab world, started a visit to Egypt and will also visit Tunisia and Libya, two other countries where popular uprisings have ousted autocratic leaders. (AP Photo/Amr Nabil, Pool)
Hoto: AP

Shugaban majalisar mulkin Soji a Masar ya faɗa wa kakakin majalisa Sa'ad al-Katatni cewar, zai gudanar da garon bawul a gwamnati gabannin zaɓen shugaban ƙasar da zai gudana a watan gobe. Wannan sanarwa ta Field Marshal Hussein Tantawi, ta zo ne bayan da majalisar Masar dake da rinjayen jam'iyar 'yan uwa musulmi, ta dakatar da zama na mako guda, bisa ga ƙorafin sojoji sun ƙi mika wa jam'iyyarsu ragamar gwamnati. Zaɓen 'yan majalisar dokoki daya gudana a watan Janairu dai, ya ba wa jam'iyyu biyu masu kishin islama gagarumin rinjayen kashi biyu daga cikin uku na kujeru 498 dake majalisar Masar. Tun bayan nan ne reshen siyasa na 'yan uwa musulmi, ya fara matsin lamba wa majalisar mulkin sojin ƙasar, data mika musu ragamar shugabancin gwamnati. Sai dai majalisar sojin data karɓi mulki tun bayan hamɓarar da gwamnatin Hosni Mubarak a ranar 11 ga watan febrairun bara, na ci gaba da goyon bayan gwamnatin priminista Kamal al-Ganzuri. Ganzuri dai ya kasance minista a karkashin mulkin Mubarak, mutumin da masu kishin Islaman suka zarga da zagon juyin juya halin daya gudana a ƙasar.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdullahi Tanko Bala