Zabe a kasar Bama
November 7, 2010A kasar Bama,an fara kada kuri´ar zaben yan majalisun dokoki, a cikin tsatsauran matakin tsaro.
Kimanin mutane miliyan 30 ne ya cencenta su kada kuri´a, a wannan zabe irin sa na farko a cikin shekaru 20 da su ka gabata.Saidai sojojin da ke rike da ragamar mulki a kasar, sun haramtawa Aung San Suu Kyi ,shugabar yan adawa shiga wannan zabe.
Kuma babbar jam´iyar adawa ta yi kira ga magoya bayanta, su kauracewa zaben.
Kasashen Faransa, Britaniya, da Italiya, sun yi hannunka mai sanda, ga turawan da ke bukata zuwa Birma a cikin yan kwanakin nan , saboda hasashen gurbacewar harakokin tsaro.
Wannan kasa dai na cikin mulkin soja, tun shekara 1962.
Tunni dai Kasashen yammacin duniya sun bayyana kin amincewa da sakamakon zaben, wanda a cewar ba zabe ne ba na demokradiya.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Ahmad Tijani Lawal