Zabe a tsakiyar yaki da 'yan tarzoma a Najeriya
March 27, 2015Za mu fara sharhunan jaridun na Jamus ne da tarayyar Najeriya.
A labarin da ta buga mai taken kuri'a tsakanin zabi guda biyu maras kyau, jaridar Neue Zürcher Zeitung cewa ta yi a tsakiyar yaki da masu ta da kayar baya na Islama, Najeriya tana gudanar da zaben shugaban kasa. Ta ce zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki ya bambamta da na baya, kasancewa masu zabe fiye da miliyan 69 suka cancanci kada kuri'a. Sannan tun bayan da kasar ta koma bin tsarin demokradiyya a shekarar 1999, ba a taba samun wani zabe da manyan 'yan takarar suka yi kankankan kamar a wannan karo ba. Masu iya magana dai kan ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.
Boko Haram ta yi awon gaba da daruruwan mutane
A labarin da ta buga a wannan makon jaridar Berliner Zeitung ta labarto cewa Boko Haram ta sace daruruwan mata da yara a lokacin da mayakan kungiyar ke tserewa daga garin Damasak. Jaridar ta ce mazauna garin da a cikin watan Nuwamban bara ya fada hannun masu ta da kayar bayan, sun ce 'yan Boko Haram sun yi awon gaba da mata da yara kimanin 400, lokacin da sojojin Chadi da janhuriyar Nijar suka kwace garin. Jaridar ma ta rawaito wani dan kasuwa na cewa yawan mutanen da Boko Haram din ta yi awon gaba da su ya kai 506, kuma ma an kashe da yawa daga cikinsu lokacin da masu fafatukar da sunan addini ke tserewa daga garin. A cikin watan Afrilun shekarar 2014 Boko Haram ta yi garkuwa da 'yan matan makarantar sakandaren Chibok kusan 300, kuma har yau ba a ji duriyar mafi yawa a cikinsu ba.
Koyan darasi daga annobar Ebola
Ita kuwa jaridar die Tageszeitung ta mayar da hankali ne a kan alkalluman da aka bayar baya-bayan nan game da cutar Ebola.
Ta ce an kusan shawo kan annobar cutar Ebola a yammacin Afirka, inda ake samu raguwar yawan masu kamuwa da cutar a kasashen Laberiya da Saliyo da kuma Guinea. Ta ce idan aka kwatanta da watanni shida baya lokacin da a kullum kusan mutane 100 ke kamuwa da cutar, to lalle an samu saukin lamarin yanzu. To amma duk da haka kungiyar agaji ta likitocin duniya wato Medicin Sans Frontiere, wadda ke gaba-gaba wajen yaki da yaduwar cutar Ebola a yammacin Afirka ta zargi kasashen duniya da jan kafa wajen ba da taimakon gaggawa don ceto rayukan mutane. Ta ce ya zama dole duniya ta koyi darasi daga wannan annoba.
Shekaru shida a gidan maza ga Karim Wade
Hukuncin daurin shekaru shida a kurkuku inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai tsokaci ga shari'ar da aka wa Karim Wade dan tsohon shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade bisa samun shi da laifin azurta kanshi da kanshi a lokacin da yake rike da mukamin minista. Kotun ta musamman da ta yi zaman sauraron shari'ar a birnin Dakar ta kuma ci Karim Wade tarar Euro miliyan 210. Hukuncin ya kuma zo ne daidai lokacin da babbar jam'iyyar adawa a kasar ta zabe shi a matsayin wanda zai yi mata takarar shugabancin kasar yayin wani taro da ta yi a karshen mako.