Zabe zagaye na biyu a Tunisiya
October 13, 2019Talla
A wannan Lahadin ne al'umar kasar Tunisiya ke zaben shugaban kasa zagaye na biyu, inda batun tsare dan takara Nabil Karoui ke ci gaba da zama abun muhawara, duk da cewar an sake shi ranar Larabar da ta gabata.
An dai kame shi tun da farko bayan sake bayyanar ayyukan ta'adda da aka alakanta da masu tsattsaurar ra'ayi.
Wanda ya yi nasara a zaben zai gaji matsalolin tattalin arziki da na rashin ayyukan yi da yanda za a iya shawo kan rigingimun tsaro.
Galibin 'yan kasar dai na sa ran ganin sauyi cikin gaggawa daga halin da ake ciki a yanzun.