Zabe zai gudana a watan Yuli a Somaliya
May 27, 2021Talla
'Yan siyasa a Somaliya sun cimma yarjejeniyar gudanar da babban zabe a kasar bayan tata-burza kan rikicin zaben a watannin da suka gabata. Firaiministan kasar Mohammed Hussein Roble da wakilan jihohun kasar biyar sun sa hannu kan yarjejeniyar yau Alhamis (27.05.21) a birnin Mogadishu.
Yanzu haka dai an tsara gudanar da zabukan 'yan majalisar dokoki da kujerar shugaban kasa a watan Yuli. Sai dai kafin a kai ga cimma wannan mataki dai, an kai ruwa rana bayan da shugaban kasar Mohamed Abdullahi Farmanjo ya tsawaita waa'din mulkinsa zuwa shekaru biyu, matakin da 'yan adawa suka yi watsi da shi tare da samun goyon bayan Amirka da kungiyar Tarayyar Turai EU.