1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben 2019 kalubalen APC tun a fidda gwani

November 2, 2018

Kama daga Zamfara ya zuwa Ogun da jihar Imo dai daga dukkan alamu gwamnonin jihar ba su ji da dadi a wajen shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole da ya sa kafa ya yi fatali da zabin gwamnonin.

Nigeria Muhammadu Buhari in London
Zaman Shugaba Buhari da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC a LondonHoto: Reuters/Nigeria Presidency

A can cikin hukumar zaben Najeriya ta INEC daukacin jam'iyyun tarrayar Najeriya  da ke shirin taka rawa a zabukan 2019 da ke tafe dai na kokarin mika sunaye na 'yan takara da nufin cika umarnin hukumar zaben tarrayar Najeriya ta INEC da ta ce Juma'a ranar karshe ce ta mika masu takara na kowane mukami na siyasa.

To sai dai kuma a cikin gidan APC mai mulki rikicin ne yaki ci yaki cinyewa a tsakanin manyan 'yan jam'iyyar da ke cigaba a cikin nunin yatsa  a tsakanin manyan 'ya'yan jam'iyyar a bisa batun na tsaida masu takara.

Rochas Okorocha gwamnan Imo da ke fiskantar tirjiya a APC matakin kasaHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Kama daga Zamfara ya zuwa Ogun da jihar Imo dai daga dukkan alamu gwamnonin jihar ba su ji da dadi a wajen shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole da ya sa kafa ya yi fatali da zabin gwamnonin.

Abun kuma da ya tada hargitsin da ya kai har ga shugaban kasar da nufin neman mafitar matsalar da ke iya kaiwa ga zama barazana mai girma a cikin jam'iyyar da ke neman dorawa a cikin nasarorinta na baya.

Rochas Okorocha dai na zaman gwamnan Jihar Imo da kuma ya kalli shugaban jam'iyyar mantawa da surukin da ya zaba domin gadonsa a bisa gadon mulkin jihar ta Imo kuma daya tilo daga sashen na Kudu maso Gabshin Najeriya cikin jam'iyyar ta tsintsiya.

Hoto: DW / Abdulkareem Baba Aminu

Tafiya zabe a cikin halin rudu ko kuma kokarin cika burin son rai dai sababbin rigingimun na iya rikidewa ya zuwa jerin shari'u da kila ma tawaye a tsakanin 'yan jam'iyyar.

To sai dai kuma a fada ta shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole APC na fuskantar sauyin yanayi na siyasa daga masu takama da ubangida a Abuja ya zuwa jam'iyyar da ke takama da farin jinin 'yan jam'iyya kafin dama ta takara a cikinta.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani