Zaben Afrika ta Kudu: Zuma ya daukaka kara kan shiga zabe
April 2, 2024Hukumar zaben kasar Afrika ta Kudu ta ki tantance Mr. Zuma mai shekaru 81, da ke neman takara a wata sabuwar jam'iyya da ya shiga mai suna uMkhonto we Sizwe (MK), bayan raba-gari da tsohuwar jam'iyyarsa ta ANC mai mulki da kuma batun raina kotu a 2021.
Karin bayani: Tsohon shugaban Afirka ta Kudu ya tsallake rijiya da baya
Za a gudanar da babban zaben shugaban kasar a watan ranar 29 ga watan Mayun wannan shekara, da hakan ke kasancewa zabe mafi daukar hankali tun bayan da kasar ta koma kan gwadaben dimukradiyya a 1994.
Karin bayani: Kotu ta sake daure tsohon shugaban Afirka ta Kudu
Shugaba Jacob Zuma da ya mulki kasar ta Afrika ta kudu daga 2009 zuwa 2018, ya gaza komawa kan karagar mulki sakamakon zarge-zargen cin hanci da karbar rashawa da kuma almubazzaranci da dukiyar kasa.