1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Amirka na kada kuri'unsu

November 3, 2020

Milyoyin Amirkawa suna ci gaba da kada kuri'unsu a duk jihohin kasar guda 50, a kokarin da suke yi na ganin kuri'unsu sun samu shiga kafin a rufe runfunan zabe nan da wasu sa'o'i.

Kombobild | Donald Trump und Joe Biden
Wa zai lashe zaben Amirka Trump ko Biden? Kuri'u za su tantance

A ziyarar gani da ido da DW ta kai wasu cibiyoyin kada kuri'u guda biyu da ke yankin Washington da jihar Maryland a kasar ta Amirka, yayin da wata jami'ar zabe mai suna Ms. Brown ta shaidar da cewa a wurinsu komai na tafiya kalau, a daya cibiyar zaben kuwa labari ya dan sha bam-bam, kamar yadda wani saurayi mai suna Joshua ya bayyana: "Wasu daga cikin mutanen da suke yi wa 'yantara yakinn neman zabe sun ci mutuncinmu sosai, amma ba za su iya dakatar da mu ba."

Karin Bayani:Amirka na bikin samun 'yancin kai

Manyan batutuwan da za su fi daukar hankali a zaben, musanman a jihohin raba gardama da 'yan takara Donald Trump da Joe Biden suke kokawar samun galaba, irinsu Florida da Pennsylvania da Michigan, sun hada da yadda sababbin injunan kada kuri'a suke yin aiki da sarrafa kuri'un da aka aiko ta gidan waya da kirga su, kuri'un da mai yiwuwa za a soke su da kuma kararrakin da za su biyo bayan zaben.

Babban mai shari'a na Pennsylvania Josh Shapiro ya ce: "Idan har wasu suka shigar da karin kararraki kan zaben, a shirye muke mu kare 'yancin jama'a na kada kuri'a, sannan mu tabbatar cewa an kirga dukkan halastattun kuri'u."
Yayin da ake kyautata zaton zuwa wajen asubah agogon na Washington, dan takarar Demokrats Joe Biden zai yi tsokaci game da zaben, shi kuma Shugaba Donald Trump ya kudiri yin liyafar daren zabe a fadarsa ta White Hause. Kwamishiniyar hukumar zabe ta tarayya Ellen Weintrau ta yi hannunka mai sanda game da samun sakamon zaben tana mai cewa: "Ba mu taba samun sakamakon zabe a hukumance a ranar zabe ba. Hakan yana wakana ne wasu makwanni daga bisani, kuma hakan ne ake yi a kowane zabe."

Karin Bayani: Wacece Kamala Harris?

Gumurzu tsakanin Trump da BidenHoto: NurPhoto/picture alliance

Ta yiwu kwamishinar zabe Weintrau tana yin kashedi ne a fatakaice, musanman duba da zargin da ake yi cewa Shugaba Trump ka iya neman a dakatar da ci gaba da kidaya kuri'u, tun kafin a kammala kirga su. Dantakara dai na bukatar kujeru 270 daga cikin 538, kafin ya zama shugaban kasar ta Amirka. Haka ne ya sa jihohin raba gardama irinsu Florida mai kujeru 29 da Pennsylavia mai kujeru 20, suka zama tamkar wasu sababbin zawarawa sakin wawa masu abin hannu da wadannan manyan masu zawarci biyu, wato Trump da Biden suke gwada kwanji sosai a cikinsu. Duk da yake akasarin jama'a suna ci gaba da hidimomin neman abincinsu na yau da kullum, amma an tsaurara matakan tsaro a wurare dabam-dabam, yayin da wasu masu shaguna suka ki budewa, saboda suna fargabar barkewar tarzoma, bayan an fitar da sakamakon zaben.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani