1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden ya zama sabon zababben shugaban Amurka

November 7, 2020

Dan takarar jam'iyyar Demokrat Biden ya yi kira ga Amirkawa da su hada kansu domin kauce wa bacin rai a daidai lokacin da abokin takararsa Donald Trump ke zargi an tabka magudi.

US-Wahl 2020 | Unterstützer von Joe Biden feiern
Hoto: Kevin Lamarque/REUTERS

Wannan dagewa da Trump yake yi, tana zuwa ne, daidai lokaci da tauraruwar babban mai hamaiya da shi Joe Biden ke kara haskawa, musanman bayan alamomi da kamfanin AP ke bayyanawa suka nuna ya sha gaban Shugaba Donald Trump a yawan kuri’u a jihar Pennslyvania mai kujeru 20, a daidai lokacin da akeci gaba da kirga kuri'un zaben lamarin da ke iya datse hanyar da Trump zai iya ci gaba da mulki bayan shekaru hudu.

Maiyuwa babban dalilin da ya sa shugaban Amirka ya kasa fahimtar karatun kurma game da yadda dimukuradiyyar da ta ba shi mulkin, ita ce kuma za ta hana shi sake cin zaben shi ne, yadda wasu na hannun damarsa irinsu shugaban ma’aikatan fadar White House Mark Meadows da Sanata Lindsey Graham suke na marawa zargin yin  magudi.

Hoto: Chip Somodevilla/Getty Images

Karin Bayani : Zaben Amirka ya bar baya da kura

Irin wannan yanayi yana da hatsarin gaske duba da yadda ‘yan gani kashenin goyon bayan Trump suke yarda da dukkan abinda yake fada, kamar yadda suka yi cincirindo da makamai a wata daya daga cikin cibiyoyin kirga kuri’u dake jihar Arizona suna ma su cewa "Ba mu damu da wanda ya kada kuri’a ba, mun fi damuwa da wanda yake kirga su."

Shi kuwa Lauyan jam’iyar Donald Trump ta Republican, Benjamin Geinsburg yana ci gaba da jefa ayar tambaya ne, game da sahihiyar hanyar da shugaban yake ganin zai iya canja sakamakon zaben, ko kuma ya yi galaba daga karshe inda yake cewa "Hanyar gaskiya ita ce, a iya samo shedu daga jihohi da za su nuna cewa an yi magudi, wanda hakan zai jefa tababa a sakamakon zaben. Kuma ya zuwa yanzu babu abinda ya nuna hakan."

Hoto: Carlos Barria/REUTERS

Yayin da Shugaban Amirka Donald Trump ya ce shi yai nasara kuma ya shiga rudu, shi kuwa mai hamaiya da shi na jam’iyar Joe Biden ya fara shirye-shiryen jawabin da zai yi idan nan da wasu ‘yan kwanaki an tabbatar masa cewa, ya lashe zabe. Kazalika, majiyoyi daga cibiyar kemfe dinsa a jihar Delware sun ce, har ma Biden ya fara hada ayarin da zai wakilce wajen harkokin karbar mulki daga gwamnatin Donald Trump zuwa jam’iyarsa. An kuma kara adadin jami’an tsaro na farin kaya da ke tsaron lafiyarsa da mukarrabansa.