Zaben Amirka: Trump ya sha alwashin tuhumar Biden
January 9, 2024Jawabin na Donald Trump, na zuwa ne a dai-dai lokacin da lauyoyinsa ke fadi tashin kare shi daga tuhume-tuhumun da ake masa na hannu a yamutsin da ya wakana a majalisar dokin kasar a shekarar 2020.
Shugaban dai ba shi da hurumin yin magana ko kuma kare kansa, kasancewar lauyoyin da ke kare shi sun gabatar da bukatar watsi da tuhume-tuhumen da ake yi wa Trump a gaban alkalan kotunan tarayyar guda 3, kafin a kai ga batun yanke hukunci a watan Maris.
Ma'aikatar shari'ar Amurka ta fitar da matsayar cewa ba za a tuhumi shugaban da ya aikata wani laifi ba a lokacin da ya ke kan karagar mulki, inda shima Trump ya bukaci amfani da wannan doka wajen wanke shi daga dukkan zarge-zargen da ake masa.
Trump, ya jaddada cewa idan har ya kai labari a zaben shugaban kasa na watan Nuwambar wannan shekara ta 2024, tabbas sai ya gurfanar da Biden a gaban kuliya.