Amirka: Rudani yayin kirga kuri'u
November 5, 2020![US Wahl 2020 Donald Trump](https://static.dw.com/image/55504539_800.webp)
Talla
A Amirka an samu jinkiri a yayin bayyana sakamakon wanda ya samu nasara a zaben shugaban kasa. Tun ba a yi nisa wajen kidayar kuri'un ba Shugaba Donald Trump y bayyana cewa ya lashe zaben wanda hakan ya sabawa ka'idojin tsarin dimukuradiyya, a yayin da abokin hamayyarsa Joe Biden ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu su jira har a bayyana wanda yayi nasara a zaben.