1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angola ta shiga sarkakiya bayan kammala zabe

Mouhamadou Awal Balarabe ZUD/AS
August 26, 2022

Jaridar Neues Deutschland ta Jamus ta ce duk da jam'iyyar MPLA da ta kwashe shekaru 47 tana mulkin Angola na da tabbacin samun nasara a zaben shugaban kasa, amma salon mulkinta ya karfafa adawa a kasar.

Angola Wahl 2022
Hoto: Lee Bogata/REUTERS

Jaridar Neues Deutschland ta mayar da hankali kan zaben gama gari da ya gudana a Angola, bisa taken "Matasa masu kada kuri'a sun kasance masu nuna sabuwar alkiblar da kasar za ta fuskanta". Sharhin ya yi nuni da cewa jam'iyyar MPLA mai mulki na fuskantar matsalar tsadar rayuwa tare da fuskantar sha'awar canji daga talakawa, saboda haka ne zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin Angola ya kasance mafi sarkakiya a tarihin kasar.

Jaridar ta kara da cewa wannan zabe da ke zama na biyar a tarihin Angola ya fi na kowane lokaci muhimmanci, duk da cewa ‘yan adawa sun yi shirin jeka-na-yi-ka na gudanar da mulki, yayin da jam'iyya mai mulki ba ta da niyar sauka daga mulki. Neues Deutschland ta ce hatta rajistar masu kada kuri'a na cike da alamun rashin gaskiya, lamarin da ke nuna cewa hukumar zabe ta kasa ta nuna fifiko ga bangaren da ke mulki. Sai dai matasan da ke goyon bayan gamayyar jam'iyyun adawa uku ne karkashin jagorancin Unita ba su bada kai bori ya hau ba, saboda sun kudiri aniyar daga murya a wa'adi na gaba don a share musu hawaye game da zaman kashe wando da ya yi musu katutu.

Shugaban Angola Joao Lourenco mai muradin yin tazarceHoto: AP Photo/picture alliance

A bangaren rikice-rikice da Afirka ta yi kaurin suna a kai kuwa, jaridar Die Tageszeitung ta ruwato cewa "Yakin basasa ya sake barkewa a Habasha". Cikin sharhin nata ta ce bayan wasu watanni na kwanciyar hankali a Habasha,  yakin basasa tsakanin gwamnatin Abiy Ahmed da masu rajin ballewa na yankin Tigray da ke arewacin kasar ya sake tashi. Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa sassan da ke gaba da juna sun yi amfani da manyan makamai a birnin Kobo, sannan fada ya kazanta a sassa da dama a wannan yanki.

Jaridar ta kara da cewa tun a watan Nuwambar 2020 aka fara gwabza fada tsakanin dakarun gwamntin Habasha da masu neman ballewa na TPLF, ko da shi ke yunkurin diflomasiyya ya sa kura ta lafa na wani lokaci. Bangarorin biyu sun amince da tattaunawar zaman lafiya, amma 'yan awaren Tigray na ganin sulhun kungiyar AU bai cire musu kitse a wuta ba. Die Tageszeitung ta ce bangarorin biyu ba su kama hanyar warware rikicin da ke tsakaninsu ba: Hasali ma yayin da 'yan Tigray ke neman a dage shingen da aka yi wa yankinsu a matsayin matakin farko na fahimtar juna, ita kuwa gwamnatin Habasha na neman fara kwance wa 'yan aware damarar yaki.

Shugaban Habasha Abiy Ahmed mai yaki da mayakan TPLFHoto: Tiksa Negeri/REUTERS

Ita kuwa jaridar Die Zeit ta yi tsakaci ne kan takun saka da Mali ke ci gaba da yi da kasashen Yamma a karkashin sharhi mai taken "mafitar karshe a Mali". Ta ce Kungiyar Tarayyar Turai EU ta gaza cimma burinta na yakar ta'addanci tare da mayar da kasar tsintsiya madaurinki daya. Amma ta karkata akalarta zuwa Jamhuriyar Nijar da niyyar sauya kamun ludayinta.

Sharhin ya ci gaba da cewa Faransa da sauran kasashen Turai sun kwashe sojojinsu daga Mali bayan tsamin dangantaka da ake fama da shi tsakanin Paris da Bamako. Wannan ya sa kungiyoyin jihadi masu alaka da al-Qaeda ke samun karfi a yankin na Sahel. A halin yanzu dai rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr na da dakaru 1100 da ke jibge a Mali, amma sabanin da ya taso ya sa fadar mulki ta Berlin ta tura sojojin nata zuwa Yamai. Jaridar ta dasa ayar tambaya ta na mai cewa, me ya sa abubuwa za su bambanta ga EU a Jamhuriyar Nijar fiye da Mali? Sannan ta amsa tana mai cewa tabbas akwai matsalar cin hanci da rashawa. Amma gwamnatin Nijar na son samar da ci gaba ga al'ummarta kuma tana son hada kai da jami'an Turai wajen magance kalubalen tsaro. A yanzu dai ta yanke shawarar yin nazari duk bayan watannin shida kan yadda ayyukan ke gudana.

Shugaban Kwango Felix TshisekediHoto: Arsene Mpiana/AFP/Getty Images

A karshe, jaridar Handelsblatt ta yi sharhinta mai taken "Doguwar inuwar Chaina a Kwango". Ta ce wannan kasa ta tsakiyar Afirka na da dimbin arzikin ma'adinan karkashin kasa. Sannan sha'awar kasashen Yamma na karuwa a Kwango, amma Chaina da ke da karfin tattalin arziki ta samu gindin zama. Fadar mulki ta Beijing na zuba biliyoyin kudi a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwongo na hannun jari a fannoni dabam-dabam. Dama kasar ta Kwango na da sama da kashi 71 cikin 100 na ma'adinan Cobalt na duniya, wanda ake matukar bukata wajen habakar motoci da ke amfani da lantarki. Yanzu haka dai, Turai na neman mafita ga albarkatun fetur da gas na Rasha, saboda haka ne kamfanonin kera motocinsu ke dada kutsa kai a Kwango don kulla kawance da gwamnatin Kinshasa.