1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Botswana ya dauki hankalin Jaridun Jamus

November 8, 2024

Sauyin gwamnati a Botswasna bayan shekaru 58 na mulkin shugaban Mokgweetsi Masis

Botswana UDC Präsidentschaftskandidat Duma Boko
Hoto: Monirul Bhuiyan/AFP

Jaridun sun nuna Botswana ta kare martabarta ta kasancewa klasa mai kwanciyar hankali da ke bin tafarkin dimukuradiyya. Tsohuwar kungiyar gwagwarmayar kwatar yanci ta amince da shan kaye. Ba kasafai ba ne jama'ar Botswana su ke ganin shugabansu cikin yanayi na juyayi da damuwa ba. Sai dai shugaban Mokgweetsi Masisi a jawabin da ya yi wa al'umar kasar ta akwatunan talabijin, cikin girmamawa da kankan da kai yace "Ina alfahari da dimukuradiyyar mu ina kuma taya dan takarar adawa murnar lashe zabe da sakamakon da ya samu".

Hoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

Jam'iyyar Masisi Botswana Democratic Party ta kwashe shekaru 58 ta na mulkin kasar tun lokacin da ta sami 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Burtaniya. Sai dai kamar yadda sakamakon zaben ya nuna Jam'iyyar ta sami kujeru hudu ne kacal a majalisar dokoki inda ta kasance ta hudu. Kawancen jam'iyyun adawa karkashin inuwar jam'iyyar sauyi ta Democratic Change UDC ta sami gagarumin rinjaye kuma dan takararta Duma Boko ya zama sabon shugaban kasa.

Tsawon lokai mutane sun kosa da gwamnatin rashin aiki, kantar talauci da tabarbarewar tattalin arziki wanda yan adawa suka ce gwamnatin ta yi almubazzaranci a kasar da ke da azikin lu'ulu'u.

Sabon shugaban kasar Botswana Duma Boko na Jam'iyyar UDCHoto: Monirul Bhuiyan/AFP

Sabon shugaban kasar Duma Boko mai 54 da haihuwa ya sami tagomashin Jama'a, Gogaggen dan fafutukar kare hakkin bil Adama ya rubuta a shafinsa na Facebook cewaa yanzu chanji ya zo ga Jama'ar Botswana su hada kai don ci gaban kasa. Ana kallon Botswana a matsayin daya daga cikin kasashen da ke da kwanciyar hankali na dimukuradiyyar a nahiyar Afrika.

Ita kuwa Jaridar die tageszeitung ta rubuta sharhinta ne akan matasa da aka gurfanar a gaban kotu a Abujan Najeriya kan zargin cin amanar kasa.

Jaridar ta ce hotunan da aka nuna a akwatunan talabijin na cikin kotun ta Abuja ya nuna yaran zazzaune a kasa cikin galabaita. Da yawa daga cikin su babu kuzari a jikinsu yayin da  hudu suka suma. Alkalan wadanda su kansu suka rude nan da nan suka dakatar da shari'ar ta matasan 76 da aka gurnar wasu ma yan shekaru 12 da haihuwa. An kama su ne tun a ranar 3 ga watan Augusta lokacin da yan sanda suka yi amfani da karfin tuwo wajen tarwatsa gangazanga da gwamnati.

Matasan Najeriya da gurfanar a kotu kan zargin cin amanar kasaHoto: Uwais Abubakar Idriss/DW

Mutane 21 ne suka rasu a zanga zangar yayin da aka tsare mutane 700 daga cikin su aka tuhumi 119 da laifin cin amanar kasa.

Najeriya ce dai kasar daya tilo a duniya da ke daure yara masu karancin shekaru kamar 'yan shekaru bakwai da haihuwa. An tuhumi matasan ne da cin amanar kasa saboda zargin cewa wasu ne daga kasashen waje suke amfani da su domin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.

Mujallar Weltplus a sharhinta mai taken Jamus na samar da kudi China na ginawa a inuwar taimakon raya kasa.

Jaridar ta ce Jamus na ci gaba da samar da miliyoyin kudade na gina tashar samar da wutar lantarki ta hasken rana da tituna a Namibia to amma kamfanonin Jamus ko wani bangare na tattalin arzikinta baya taka rawa a ayyukan, maimakon haka China ce ta ke samun kwangila daya bayan daya kuma rashin jin dadin na kara baiyana karara.

Hoto: Thomas Imo/photothek/picture alliance

Mujallar ta ce Jamus na fuskantar barazanar koma bayan tattalin arziki, matsakaitan kamfanoni kamar kamfanin motoci na Volkswagen  da kamfanin BASF mai yin Batura da kamfanin kere kere na Thyssenkrupp suna rage dubban ma'aikata ko ma rufe wasu rassan su baki daya. Amma a daya bangaren gwamnatin tarayya ta na nuna bajinta duk da matsalar tattalin arzikin da ta ke fuskanta a cikin gida ta na tallafa wa harkokin kasuwancin wasu a kasar waje. Jaridar ta ce Jamus na gina tashar wutar lantarki mai karfin Megawatts 100 na makamashin Solar a Namibia inda ta zuba tsabar kudi sama da euro miliyan 83 wanda kudin yana tafiya ne kai tsaye ga China saboda kamfanin da ke kwangilar aikin na China ne. Jamus ba ta amfana da komai ba saboda babu kamfanonin Jamus a Namibia da za su nemi kwangilar aikin).