1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Cece-kuce bayan zaben Cote d'Ivoire

Suleiman Babayo
November 1, 2020

Jam'iyyun adawa na Cote d'Ivoire sun yi kira da a samar da wata gwamnatin farar hula ta wucin gadi saboda wa'adin Shugaba Alassane Ouattara ya kawo, domin rashin yarda kan zaben da ya wakana.

Elfenbeinküste | Präsidentschaftswahlen | Ausschreitungen in Abidjan
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Mutane da dama sun halaka sakamakon rikicin da ya biyo bayan zaben kasar Cote d'Ivoire kamar yadda hukumomi suka tabbatar kuma galibin tashe-tashen hankula a wuraren da 'yan adawa ke da karfi. Zaben da ake gani Shugaba Alassane Ouattara zai lashe.

Zaben wanda Shugaba Ouattara mai shekaru 78 da haihuwa ke neman ta'azarce a wa'adi na uku na madafun ikon kasar abin da 'yan adawa ke gani ya saba kundin tsarin mulki. Kimanin mutane 30 suka halaka sakamakaon tashe-tahsen hankula gabanin zaben yayin da wasu kuma suka gamu da ajalinsu bayan zaben.

Mutane da dama dai na fargabar sake koma gidan jiya na irin wannan riki inda manyan yan siyasar da ke hamaiya da juna ke neman tunzura tarzoma. 'Yan adawa a kasar Cote d'Ivoire sun kira da a samar da wata gwamnatin rikon kwarya ta wucin gadi da zata kai kasar ga gudanar da manyan zabuka ciki haske da adalci. Kakakin 'yan adawar Pascal Affi N'Guessan ne ya bayyana haka.

Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Tun farko jagoran 'yan adawa kana tsohon shugaban kasar Henri Konan Bedie ya nemi kauracewa zaben da kuma nuna tuirjiya daga mutanen kasar. A daya bangaren tsohon jagoran 'yan tawaye kana tsohon Firaminista Guillaume Soro ya fito a kafofin sada zumunta na intanet yana cewa daga yanzu ba za su mutunta a matsayin Alassane Ouattara na zama shugaban kasar.

Tuni Majalisar Dinmin Duniya ta yi kiran kwantar da hankula tare da bukatar samun zauna lafiya, a kasar da rikicin zabe ya kai ga mutuwar kimanin mutane 3000 a karshen shekara ta 2010 zuwa farkon shekara ta 2011, kuma zaman lafiya ke ci gaba da tangal-tangal a kasar ta Cote d'Ivoire da ke yankin yammacin Afirka.