Neman madafun iko a fadar Elysée ta kasar Faransa
April 22, 2022A bisa kuri'a jin ra'ayin jama'a da aka gudanar dai daga karshe Shugaba Emmanuel Macron na kan gaba da kusan kashi 10 cikin 100, amma kuma wasu na cewa ba a nan take ba. Sai dai kawai abin da sakamakon zabe ya nuna. Don haka kawo yanzu magoya bayansa ba su da wani abin fada, domin komai ya rataya ga yawan fitowar jama'a, kuma wane bangare na jama'a ne suka fi fitowa zaben. Don Haka yakin neman kujerar shugabancin Faransa a yanzu yana iya kasancewa ta ko wane bangare.
A yayin mahawarar talabjin da aka yi an yi tsammani 'yar ra'ayin kishin kasa Marine Le Pen za ta yi azarbabi kamar yadda ta faru a 2017, amma kuma sabanin haka wannan karon da alama ta shirya kafin ta shiga, kuma bayan mahawarar sunanta ya yi sama daga bangaren Faransawa.
Sai dai shi kansa Shugaba Macron, akwai alamar ya sauya ra'ayi don karkata ta inda kuri'u suke, a cewar Ariane Bogain na Jami'ar Northumbria.
Karin bayani: Macron da Le Pen a zagaye na biyu
"A bayyane yake Macron ya sauya alkibla zuwa bangaren masu sauyi, kuma hakan yana ma'ana domin samun kuri'un masu irin wannan ra'ayi, saboda daya bangaren masu ra'ayin 'yan mazan jiya bai yi masa aiki ba. Kuma ina ganin babban abin da zai iya yin tasiri shi ne yawan wadanda suka kauracewa zaben, kuma ba wai yawansu ba amma su waye ne suka kauracewa kada kuri'ar."
Muhimman batutuwan da mahawarar 'yan takaran shugaban kasar ta Faransa a talabijin, sune sake tsarin kudin fansho, yakin Ukraine da Rasha, batun kare muhalli har izuwa batun daura dan kwali ga mata Musulmi.
Daga karshe dai Emmanuel Macron aka bayyana a matsayin wanda ya yi nasara a mahawarar da kashi 59 cikin 100, amma masu lura da siyasa suka ce sakamakon mahawarar talabijin ba shi ne zai iya tabbatar da kuri'un da dan takara zai samu ba a cewar Ariane Bogain.
"Ina ganin akwai daure kai game da muhimmancin mahawarar 'yan takarar, yadda wasu ke kallonta a matsayin karshen komai. Amma kuma bincike ya nuna mahawarar, daya ne a cikin wasu bangagrori masu yawa na sakamakon zabe. Shin Le Pen ta fadi zaben 2017 don tabargaza da ta yi a mahawara? Sam babu, shin mummunar mahawarar ta taimaka a faduwarta zabe? E, domin ta karfafa tunanin jama'a cewa ba ta kasance mai gaskiya ba."
Babbar matsalar shugaba Macron dai shi ne tsaffin jam'iyyun kasar da magoya bayansu, ko da shi ke a baya-bayan nan tsaffin shugabannin Faransa biyu Francois Hollande da Nicolas Sarkozy duk sun nemi a kadawa Emmanuel Macron kuri'a, amma kuma ayar tambaya ita ce shin suna da masu sauraronsu? Ita kuwa Marine Le Pen, shugabannin Turai na yi mata kallon babbar barazana ga Tarayyar Turai da kungiyar tsaro ta NATO, don haka masu wannan tunanin suma sai inda karfinsu ya kare.