Zaben fidda gwani a kasar Kenya
November 17, 2007Talla
An fuskanci hautsini da rikice -rikice a lokacin zaɓen fidda gwani na ´Yan majalisun dokoki da aka gudanar jiya a Kenya.Rahotanni sun shaidar da arangama a gurare daban daban, a tsakanin magoya bayan jam´iyyu a ƙasar.Hakan a cewar bayanai ya haifar da faɗan fito na fito, a tsakanin ´Yan siyasar da kuma Jami´an tsaro a ƙasar.Babu dai wanda ya rasa rai to amma an ce da yawa sun jikkata. Ana sa ran gudanar da zaɓen ´Yan Majalisun dokokin ne da kuma na shugaban ƙasa, a ranar 27 ga watan Disambar wannan shekara.