1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Cancanta ko kudi a zaben fidda gwani?

Uwais Abubakar Idris AMA(ATB)
June 9, 2022

Zaben fidda gwani tsakanin 'yan takara ya bullo da sabon salo a siyasar Najeriya, inda wasu ‘yan takara duk da ficen da suka yi a yankunana da dama, sun kasa samun ko da kuri’a daya.

Hotunan 'yan takara | Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar
Hotunan 'yan takara | Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso da Atiku Abubakar

Zaben fidda gwani na jamiyyar APC mai mulki a Najeriya ne dai aka fi ganin wannan sabon salon a siyasar Najeriyar, inda wasu ‘yan takarar da ake kalon suna da tagomashi amma suka kasa samun ko da kuri’a daya. Alall misali Sanata Rochsa Okorocha duk da cewa dan kabilar Igbo ne amma a yankin arewacin Najeriya ya girma, kuma ya kasance mai alfahari da wannan yanki saboda yadda yake amfani da harshen Hausa, amma duk ya tashi baya da kuri’a ko da guda a yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar APC.

Karin Bayani: Tinubu ya lashe zaben fidda gwani a APC

Wasu 'yan siyasa kamar Dr Yunusa Tanko da ya taba tsayawa takarar shugabancin Najeriyar ya fuskanci irin wannan halin inda yace "Zaben jam'iyya ya sha ban-bam da zaben da jama’a gaba daya za su yi, idan bai bada kudi ba ya ja hankalin jama a cikin irin wannan tsarin da suka yin zabe wallahi ba zai samu kuri’a ba. Ana maganar mutum daya ya bada dala dubu 30 har da mota, to wannan ya sa su Rochas Okorocha bai samu kuri’a ba, dama Ogbonnaya Onu shi ma bai samu kuri’a ko daya ba."

Nuna karamci da kara a tsakanin al'ummar Najeriya abu ne da ake amfani da shi a fagen siyasa sosai, domin ko da matakin da wasu gwamnonin jam'iyyar APC suka dauka na dagewa kan mulki ya koma yankin kudancin Najeriya, na daga cikin batun na karamci.

Duk da haka kama daga Ogbonnaya Onu zuwa Jack Rich da Rochas Okorocha, ba wanda ya samu koda kuri’a guda a zaben, lamarin da ke kasancewa abin mamaki tattare da wannan.

Karin Bayani:  Siyasar kabilanci na son kunno kai a Najeriya

A ya yinda ‘yan takarar da suka sha kaye a zabubbukan ke nazari da koyon darasi a daukacin abin da ya faru ko ya dan takara kan ji ne idan ya fahimci yana da farin jini amma kuma ya gaza samun koda kuri’a guda daya a lokacin zaben fitar da gwani a Najeriya?

Duk da cewa a takara ta siyasa dole a samu wanda ya yi nasara da shan kaye, batun kasa samun koda kuru’a guda ga 'yan takara na aika babban sako kan makomarsa ta siyasa, musamman a yayin da ya gwada farin jininsa kuma ya masa yankar baya a siyasa da akan cewa mugun wasa.