1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Matsakan tsaro a zaben Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Uta Steinwehr | Mouhamadou Awal Balarabe SB
December 27, 2020

'Yan bindiga a yankuna da dama na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na kawo fargaba a zaben kasar inda tuni aka fara kada kuri'a musamman a birnin Bangui fadar gwamnatin kasar.

Zentralafrikanische Republik Bangui | Wahlen
Hoto: ALEXIS HUGUET/AFP

A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ana gudanar da zaben 'yan majalisa da na shugaban kasa a cikin yanayi na rashin tsaro. Masana harkokin kasa da kasa sun nunar da cewar babban muradin da wanda zai iya nasara zai saka a gaba shi ne kawo karshen rikice-rikice tare da hada kan kasar.

Yanayin tsaro ya sukurkuce a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tun bayan da 'yan takara suka fara yakin neman zaben na 27 ga Disamba. Hasalima fada ya sake barkewa tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnati a wasu yankuna na kasar, lamarin da ya kai ga sun sace jami'an hukumar zaben, tare da yi kafar angula ga aikin raba katin masu kada kuri'a. Kimanin kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai guda uku ne ke barazanar tayar da zaune tsaye matikar shugaba da ke ci yanzu Faustin Archange Touadéra ya yi magudi don samun wa'adi na biyu.

Hoto: Jean F. Koena/DW

Dama dai a 'yan shekarun da suka gabata, kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta yi fama da yakin basasa inda wasu mayakan mabiya addinin kirista da Musulmi marasa rinjaye suka gwabza fada tsakaninsu. Babu adadin mutanen da suka mutu, amma hukumar 'yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu akwai kusan' yan gudun hijira miliyan 1.3 da ba su koma matsugunansu ba. Sai dai a watan Fabrairun 2019, gwamnati da kungiyoyi da ke dauke da makamai 14 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Khartoum na Sudan, lamarin da ya taimaka wajen kwantar da kurar rikicin, a cewar Peter Knoope, wanda ke gudanar da bincike da ba da shawara ga gwamnatoci da kungiyoyi.

'Yan takara 17 ne ke zawarcin kujerar shugabancin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da ke fama da rikice-rikice ciki har da shugaba mai barin gado Faustin Archange Touadera. Sai kuma tsohuwar shugabar rikon kwarya Catherine Samba-Panza da kuma tsoffin firaministoci Anicet-Georges Dologuélé da Martin Ziguélé. Shi ma tsohon shugaban kasar François Bozizé ya so sake tsayawa takara duk da zarginshi da ake yi da daure wa kungiyoyin tawaye gindi. Amma kotun tsarin mulkin Afirka ta tsakiya ta dakatar da takararsa saboda an gurfanar da shi gaban kuliya, lamarin da ya sa shi mara wa tsohon Firaminista Dologuélé baya.

Hoto: Jeff Murphy Barès/DW

Duk 'yan takara sun yi alkawarin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali idan suka sami nasara. Dukkansu suna sukar yarjejeniyar ta Khartoum a yadda take a yanzu ko aiwatar da ita. Amma dan takara Anicet-Georges Dologuélé ya ce akwai bukatar yi wa yarjejeniyar zaman lafiya gyaran fuska.

Sai dai baya ga rikice-rikicen na cikin gida da take fama da su, wasu manyan kasashen duniya wato Faransa da ke zama tsohuwar uwargijiyar Afirka ds Tsakiya da kuma Rasha na kokarin kare muradunsu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai arzikin albarkatun kasa.

Babban kalubalen da ke gaban shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai shi ne na shigar da membobin kungiyoyin 14 da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar Khartoum cikin tsarin tafiyarwa na gwamnati domin kowa ya amfana. Sannan kuma wanda zai yi nasara yana da jan aiki a gabanshi wajen sasanta bangarorin da ke ci gaba da gaba da juna a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.