Zaben Shugaban kasa zagaye na biyu a Nijar
March 11, 2016Za dai a fafata ne tsakanin dan takarar jam'iyyar Lumana Afirka ta adawa Hama Amadou da a yanzu haka yake tsare a gidan kaso da kuma Shugaba Mahamadou Issoufou na jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki wanda ke neman wa'adi na biyu. Jam'iyyar adawar dai ta bayyana cewa zaben na rashin adalci ne kana ta zargi gwamnati da yin murdiya a zagaye na farko na kuri'un da aka kada, koda yake kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana cewa ta gamsu da yadda aka gudanar da zaben bayan da ta tura masu sanya idanu a zaben na zagayen farko.
A zagaye na farko na zaben da aka gudanar cikin watan Fabarairun da ya gabata dai, babu dan takarar da ya samu kaso 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada kamar yadda doka ta tanada, wanda hakan ya tilasta yin zagaye na biyu da za'a gudanar ranar 20 ga wannan wata na Maris da muke ciki.