1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben jihar Bavaria jan aiki gaban Angela Merkel

Abdourahamane Hassane MA
October 12, 2018

A wannan Lahadin ne za a gudanar da zaben 'yan majalisun Jihar Bavaria ta Jamus, zaben da ke da muhimmanci ga dorewar gwamnatin shugabar gwamnati Angela Merkel.

Angela Merkel da Horst Seehofer
Angela Merkel da ministan cikin gida, Horst SeehoferHoto: picture-alliance/AP/M. Sohn

Zaben wanda za a zabi ‘yan majalisun jihar su 180, a wannan karon hasashe ya nuna cewar jam'iyyar CSU mai kawancen da CDU ta Angela Merkel da a zabukan baya ta ke da karfi a Jihar, na fuskantar rasa rinjaye a majalisar jihar sakamakon barazanar da take fuskanta daga jam'iyyar masu fafutikar kare muhalli da kuma ta masu kyamar baki AfD.

Wannan zabe na da mahimmaci ga Jamus baki daya musammun game da irin yadda tafiyar gwamnatin hadaka za ta kasance da kuma aka zura ido a ga yadda zaben zai kaya. A takaice dai gwamnati na cikin tsaka mai wuya.

Wani hasashe da aka yi, ya nuna cewar jam'iyyar za ta fadi da kason da ba ta taba samu ba, na kashi 33 cikin dari a kuri‘un da za a kada. Yayin da jam‘iyyar masu fafutikar kare muhalli za ta samu kashi 18, babbar abokiyar gabar ta AfD ta masu kyamar baki. Ana ganin AfD za ta iya samun kashi 10 cikin dari na kuri‘u a zaben wacce ta kara samun magoya baya tun lokacin da gwamnatin Angela Merkel ta amince da shigowar sama da miliyan daya na ‘yan gudun hijira a shekara ta 2015 zuwa 2016 da ke kara samun amincewar jama‘ar da suka fice daga CSU.

Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

A shekara ta 2008, jam‘iyyar ta CSU ta rasa rinjaye a majalisar ta Bavaria kafin a shekara ta 2013 a zaben Jam‘iyyar ta samu kashi 48 cikin dari, abin da ya ba ta damar samun ‘yan majalisu 101 cikin 180. Sai dai yanzu kalubalen da take fuskanta na sauran jam‘iyyun na iya hana ta kaiwa ga samun rinjaye sai ta nemi kawance.

 

Masu sharhi na ganin jam‘iyyar ta CSU ta rasa kwarjinin da take da shi saboda sakamakon kawancen da ta yi da CDU, sannan kuma ana ganin irin kalamun da shugabannin jam‘iyyar suka yi a lokacin yakin neman zabe musammun jagoran jam‘iyyar Horst Seehofer da kuma firimiyan jihar Bavaria, Markus Söder, a lokacin da suka rika yin kalamu irin na ‘yan Populist domin jawo hankalin magoya bayan jam‘iyyar masu kyarmar baki.

Wannan sakamako na hasahe da aka yi muddin ya tabbata, babu shakka zai kawo matsala ga gwamnatin hadakar wacce CSU take ciki, kuma tafiyar  gwamnatin hadakar na iya kasancewa da wahala, don ana ma  ganin jagoran jam'iyyar Horst Seehofer, da wuya ya ci gaba da rike matsayi a gwamnatin ba tare da ya yi marabus ba.