Zaben Kenya: Kenyatta ya sha gaban Raila Odinga
August 9, 2017
Fitar wannan sakamako ke da wuya ne dai madugun 'yan adawar kasar Raila Odinga ya yi taron manema labarai inda ya ke cewar ba za su amince da sakamakon ba domin kuwa suna da shaidun da ke nuna cewar jam'iyya mai mulki ta tafka magudi. Wannan dai ya sanya magoya bayan Odinga a Kisumu da Nairobi fantsama kan tituna don yin zanga-zanga. Tuni dai jam'iyya mai mulki da ma hukumar zaben kasar suka nesanta kansu daga zargin magudi a zaben.
Wannan tashin hankali da aka samu dai ya sanya 'yan sanda a yin amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu boren. Masu sanya idanu a zaben ciki kuwa har da tsohon shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki sun ya yaba da sahihancin zaben inda ya ke cewar ''hukumar zabe ta yi aikinta kuma al'umma sun yi abinda ya kamata. jami'ai sun yi nasu aikin kamar yadda ya dace saboda haka a nawa ganin zan ce al'ummar kenya sun taka rawar gani, a matsayina na dan Afirka ina alfahari da su''
A zaben shekarar 2007 mutane fiye da dubu daya da dari biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon rikicin da ya biyo bayan zaben wancan lokacin baya ga wasu dubu dari shida da suka rasa matsugunansu abinda ya sa ministan tsaron cikin gida Fred Matiangi ya yi saurin yin jawabi ga al'ummar kasar da su guji tayar da zaune tsaye.
Kenyatta mai shekaru 55 na kan hanyarsa ta jan ragamar mulkin kasar ta Kenya a karo na biyu na wa'adin shekaru biyar sai dai kuma yanzu hankalin duniya ya karkata kan ko Mista Odinga ya shirya bayar da kai bori ya hau na amincewa da sakamakon zaben da ya bai wa abokin adawarsa na tsawon lokaci Uhuru Kenyatta nasara ganin fargabar da al'ummar kasar ke ciki na sake aukuwar tarzoma a wannan zaben da ke cike da takaddama.