Zaben majalisar dokokin Jamhuriyar Benin
January 9, 2026
Ana ci gaba da shirye-shiryen karshe na zaben 'yan majalisar dokokin kasar Jamhuriyar Benin, wanda za a gudanar ranar Lahadi mai zuwa. Zaben yana zuwa watan daya bayan yunkurin juyin mulkin da wasu sojoji suka yi a kasar da ke yankin yammacin Afirka.
Zabe bayan yunkurin juyin mulki
Zaben majalisar dokokin zai iya nuna inda aka aka nufa a zaben shugaban kasa da aka tsara a watan Afrilu mai zuwa. Ana sa ran kawancen jam'iyyun da ke cikin gwamnatin Shugaba Patrice Talon zai taka rawar gani lokacin zaben na 'yan majalisar dokoki. Shi dai Shugaba Talon yana wa'adin karshe na mulkin shekaru 10, bayan lashe zabe sau biyu, na wa'adin shekaru biyar-biyar kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Talon mai shekaru 67 da haihuwa hamshakin mai arziki ya taimaka wajen habaka tattalin arzikin kasar ta Jamhuriyar Benin cikin shekaru 10 da suka gabata. Amma ana zarginsa da tauye hakkin 'yan adawa a kasar.