1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP ta yi fatali da sakamakon zabe a Najeriya

February 25, 2019

A yayin da hukumar zabe ta INEC ke ci gaba da bayyana da sakamakon zabe, babbar jam'iyyar adawa PDP ta yi watsi da sakamakon zaben tana mai cewa an tafka magudi

Nigeria, ehemaliger Vizepräsident Atiku Abubakar
Hoto: Getty Images/P.U.Ekpei

A Najeriya babbar jam’yyar adawa ta PDP ta ce ta yi watsi da sakamakon zabe da ke fitowa ta na mai cewa babu sahihanci a cikinsa. Duk da cewar har yanzu ana ci gaba da tattara sakamakon da ke ftowa a matakin jihohi, a wani taron manema labarai da shugaban jam'iyyar Chief Uche Secondus ya kira, ya ce an sauya sakamakon zaben a Jihohin Sokoto da Nasarawa, sannan an yi kutse ga shafin  hukumar zaben ta INEC. Shugaban Jam'iyyar ya ce bisa wadannan dalilai da wadansu ko kadan jam'iyyar ba za ta lamunta da sakamakon ba domin tana da cikakkun sakamakon zaben da suka zo mata daga ko ina a fadin kasar. Sanarwar ta kuma zargi jam'iyyar APC mai mulki da tura manyan jami'an gwamnati cikin jihohin kasar don murda sakamakon zabe. Babbar jam'iyyar adawar ta kuma soki yadda aka kama daya adaga cikin kakakinta Buba Galadima tana mai cewar hakan na matsayin wata babbar barazana.