Zaben Netherlands a watan Oktoba
June 6, 2025
A kasar Netherlands an aka ranar 29 ga watan Obtoba na wannan shekara domin gudanar da zaben kasar sakamakon rushewar da gwamnatin kawance ta yi a farkon wannan makon. Gwamnatin ta rushe saboda jam'iyyar mai matsanancin ra'ayi ta janye goyon baya, abin da ya jefa kasar cikin rudanin siyasa.
Karin Bayani: Netherlands ta bukaci fita daga yarjejeniyar Turai kan yan gudun hijira
Ministar cikin gida Judith Uitermark ta tabbatar da saka ranar zaben Laraba 29 ga watan na Oktoba. Tuni sarkin kasar Willem-Alexander ya bukaci Dick Schoof ya ci gaba da rike mukamun firaministan gwamnatin rikon kwarya.
Ita dai kasar Netherlands ke zama ta biyar wajen karfin tattalin arziki tsakanin kasashen kungiyar Tarayyar Turai, kuma yanzu haka jam'iyyar masu ra'ayin rikau suna kara samun tagomashi a kasar.