1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Bazoum Mohamed ya lashe zaben shugaban kasa

Salissou Boukari RGB
February 23, 2021

Jam'iyyar adawa ta RDR chanji tayi fatali da sakamakon zaben shugaban kasa da ya bai wa Bazoum Mohamed na jam'iyyar PNDS Tarayya nasara, ta yi kira ga 'yan kasa da su fito suyi zanga-zanga.

Niger Wahlkampf Mohamed Bazoum
Mohamed Bazoum ya sami nasara da tazara mai yawaHoto: Facebook/Mohamed Bazoum

A Jamhuriyar Nijar yayin da bangaran dan takara Mohamed Bazoum na jam’iyya mai mulki ke nuna farin ciki dangane da nasarar da ya samu na lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da tazara mai yawa, daga nasu bangare masu goyon bayan tsohon shugaban kasar kuma dan takarar jam’iyyar RDR Chanji, Alhaji Mahamane Ousmane  bacin ransu suke nunawa inda ma suka ce sam ba za ta sabu ba wai bindiga a ruwa, ganin irin abin da suka kira aringizon kuri’u da suka ce ya gudana musamman ma a jihar Tahoua da ke arewacin kasar ta Nijar. 

Karin Bayani:  Nijar: An kammala zaben shugaban kasa

Tuni dai ga sakamakon da hukumar zaben kasar ta Nijar, CENI ta bayar ya nunar da cewa, dan takarar jam’iyya mai mulki Malam Bazoum Mohamed ne ke kan gaba da tazarar kuri’u sama da dubu dari biyar, kamar yadda sakamakon hukumar zaben ya nunar. Tuni daga bangaren dan takara Mahamane Ousmane suka ce ko kadan ba za su yarda da wannan sakamako ba, bisa zargin magudi.

An fafata a zagaye na biyu a tsakanin Mahamane Ousmane da Mohamed Bazoum

Masu goyon bayan dan takara Bazoum Mohamed na jam’iyyar PNDS ba su da wata magana illa godiya ga Allah, ganin ya yi wa 'yan Nijar zabi da ya bai wa dan takararsu mafi yawan kuri’u da tazara mai yawan gaske. Ga jimilla kamar yadda kowa ke fadi, zaben na Nijar an gudanar da shi babu wani babban tashin hankali da ya wakana a yayin zaben, amma tattara sakamakon zaben da kuma yadda aka bayar da shi ke shirin haifar da turjiya daga bangaren adawa.

Karin Bayani:  Nijar: Matakan dakile tarzoma yayin zabe

Ya zuwa yanzu dai, ana jiran hukumar zabe ne ta bayar da ragowar sakamakon kananan hukumomin da suka rage, wanda tuni a wata hira da aka yi da shi, mataimakin shugaban hukumar zaben ta Nijar CENI, ya ce sakamakon da ya rage ba zai sauya komai ba. Sai dai kuma ga labarin da muke samu an ce tuni wakillan 'yan adawa na jihar Tahoua suka ki amincewa da sanya hannunsu ga wasu takardun sakamakon na jihar inda suka ce sam ba su yarda da sahihancinsu ba.