1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: CENI ta yi taro da 'yan siyasa

Salissou Boukari LMJ
July 23, 2020

Hukumar zaben Jamhuriyar Nijar CENI ta kira wakillan jam'iyyun siyasa wani taro, domin tattauna batutuwa da suka shafi shirin zabukan da za a gudanar a kasar. Sun dai tattauna halin da ake ciki bayan kidayar masu zabe.

Niger Wahlen Unabhängige Wahlkommission (CENI)
Shirye-shiryen zabe a NijarHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Da farko dai batun takardun haihuwa ne aka yi, inda aka sanar da 'yan siyasar adadin takardın da aka yi wa jama'a da ba su da takardun haihuwa a cikin kasar ta Nijar, a wani mataki na ba su damar a kidaya su domin su yi zabe. Sai kuma daga bisani aka tabo batun ita kanta kidayar jama'ar da aka yi, inda aka bayar da adadin mutanen da aka samu kidayawa da a halin yanzu yawansu ya kai mutun sama da miliyan bakwai, wanda hakan ya ba da sama da kasao 76 na adadin wadanda ya kamata a kidaya a fadin kasar ta Nijar. Sai dai tuni wasu 'yan siyasar suka soma kokawa da abun da suka kira rashin tsari daga hukumar zaben ta CENI. 

SHirye-shiryen zabe a NijarHoto: Reuters/J. Penney

Babban abin da ya sanya wa akasarin 'yan siyasar walwala shi ne lokalin da hukumar zaben kasar CENI ta bayar na cewa za a yi zaben kananan hukumomi a ranar 13 ga watan Disamba kafin kowanne zabe, sabanin ranar 17 ga watan Janairu da hukumar zaben ta bayar a baya wanda 'yan siyasa har na adawa ba su yarda da shi ba. Wannan sanarwa dai ta yi wa akasarin 'yan siyasar dadi, ko da ya ke akwai wadanda suka nuna rashin jin dadinsu da za a yi wannan zabe kafin sauran zabuka. Amma a cewar Honorable Sanoussi Maraini shugaban riko na jam'iyyar PSD Bassira ta Marigayi minista Ben Omar da yawansu sun yi farin ciki da wannan rana ta 13 ga watan Disamba.

Sai dai a 'yan adawar sun yi halin nasu na kauracewa shiga wannan zaure na tattaunawa, duk kuwa da cewa an tattauna batun da suma suke da ja a kanshi. Amma kuma har a yau din 'yan siyasar da dama sun yi fatan ganin 'yan adawa sun dawo domin tafiya tare. Sai dai da yake magana kan burin da suke da shi na shirya zabe mai kyau a kasar ta Nijar, a cewar shugaban hukumar zabe Maitre Issaka Sounna ya ce suna aiki hannu da hannu da kungiyar Tarayya Afirka da kuma ECOWAS, inda suke sanar da su yadda tafiyar shirye-shiryen zaben na Nijar ke gudana. Sannan kungiyar OIF ta kasashen da ke magana da harshen Faransanci ta isa Nijar bisa bukatar shugaban kasar Nijar din, domin saka ido ga aikin da aka yi na kidayar masu zabe dan tantance jerin sunayen masu zaben.