Gwamnati ta yi watsi da kiran 'yan adawa na tattaunawa domin gyara matsalolin siyasar Nijar bayan zabubbukan 'yan majalisa da na shugaban kasa da Mahamadou Issoufou ya lashe.
Talla
A Jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ce ta yi watsi da wasu shawarwarin da kawancen 'yan adawar kasar ya gabatar mata a wani yunkuri na hawa kan teburin shawara don tattauna matsalolin siyasar kasar da suka barke bayan zabubbukan da suka gudana.