1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Zaben Rasha: Putin ya mika sakon godiya ga al'ummar kasar

March 18, 2024

A yayin da kasashen yammacin duniya ke Allahwadai da zaben shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a karo na shida, shugaban na Rasha ya gabatar da jawabin godiya ga dandazon magoya bayansa a birnin Moscow.

Majigin shugaban Rasha Vladimir Putin a dandalin Red Square dake birnin Moscow
Majigin shugaban Rasha Vladimir Putin a dandalin Red Square dake birnin MoscowHoto: Maxim Shemetov/REUTERS

A wani taron biki na kasaita da aka shirya a dandalin Red Square da ke birnin Moscow, shugaba Putin tare da 'yan takara uku da suka mara masa baya, ya yi jinjina ga al'ummar Rasha wajen tabbatar da nasararsa, inda ya jaddada cewa za su yi aiki tare wajen ciyar da kasar gaba.

Karin bayani: Shugaban Rasha Vladimir Putin ya lashe zaben shugaban kasa 

Jawabin na shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da ake bikin cika shekara 10 da dawo da yankin Creamea karkashin ikon Rasha daga wani bangare na tsibirin Ukraine.