Zaben shugaban kasa a pakistan
October 6, 2007Ayau ne yau yan majalisar dokoki dana yxankuna ke kada kuriunsu,a wani zabe da ake ganin zai sake baiwa shugaban mulkin sojijn kasar Pervez Musharaf ,wasu karin shekaru biyar akan karagar mulki.Ana saran cewar,jammiiyyar PML-Q,mai mulkin kasar zata fadada waadin Musharraf,duk da yin murabus da yan majalisar dokokin kimanin 200,daga cikin 1,159,da sukayi acikin wannan makon.Gabannin fara wannan zabe na yau dai,wasu yan majalisar 100,daga jammiiyyar tshohuwar prime minista mai gudun hijira Benazir Bhuto ne,suka fice daga harabar majalisar.A baya dai Bhutto tayi alkawarin cewa magoya bayan jamiiyyarta ta PPP,zasu shuga wannan zabe na shugaban kasa,bayan gwamnati tayi mata afuwa daga zargin da ake mata na cin hanci da rashawa, a ranar jumaa.Bugu ta kari Bhutto tace zata komo pakistan a ranar 18 ga wata,domin shi zaben yan majalisa da zaa gudanar kasa baki daya.