Zaben shugaban kasa a Senegal
March 25, 2012Al'umar Senegal na cigaba da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, inda ake fafatawa tsakanin shugaba mai barin gado Abdulahi Wade mai shekaru kusan 86 a duniya,da tsofan Firaministansa Macky Sall, wanda ya samu kashi 26 cikin dari a zagayen farko.
Ya zuwa wannan lokaci rahotanin sun tabatar da zaben na wakana lami lafiya,kuma kayan aiki sun wadata kamar yadda Demba Seydi shugaban wata runfar zabe ya bayyanawa Babu Diallo,wakilin sashen Faransanci na DW a Dakar babban birnin Senegal:Ya ce an kawo duk kayan zabe da ta kamata, akwatina, runfuna,takardu, da dai sauransu, sannan jami'an tsaro na bi sau da kafa domin ganin komi ya gudana ba tare da hargisti ba.
Zagayen farko ma ya wakana lami lafiya, saidai zullumin da jama'a ke hange shine,abinda zai biyo bayan bayyana sakamakon zagaye na biyu na zaben .
Baki daya 'yan takara 12 da ba su yi nasara kaiwa ga zagaye na biyu ba, sun umurci magoya bayansu su zabi Macy Sall, abinda masu kula da harakokin siyasar Senegal ke tunanin zai taimaka masa ya lashe zaben.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Halima Balaraba Abbas