1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a Saliyo

March 7, 2018

Muhimman abubuwan da 'yan adawa ke neman kuri’u, su ne cin hanci da rashawa da suke cewa ya yi kaka gida a kasar. Inda a cewarsu jam’iyya mai mulki tana ba da kwangilar ayyuka kan kudin da suka zarce hankali.

Wahlen in Sierra Leone
Hoto: DW/Abu-Bakarr Jalloh

Kandeh Yumkella, tsohon jami'in Majalisar Dinkin Duniya shi ne dan takarar shugababn kasa a karkashin jami'iyyar National Grand Coalition.

"A wannan kasar ta mu ce fa aka fadada wata hanya mai tsawon kilomita biyar a kan kudin da suka wuce dala milyan 20. Kuma babu wata gada da aka yi a titin, kawai an kara fadin hanyar ne. Zan iya baka misalan hanyoyi biyar ko shida da aka gina da irin wadannan makudan kudaden. Kuma fa bamu mance yadda suka sace dala milyan 14 ba da sunan yakar ebola  a lokacin da cutar ta kashe jamaa dubu hudu"

Ita dai jam'iyya mai mulki  ta All People's Congress, APC, tana takama karkashin mulkinta kasar ta yi kokari ta magance cutar Ebola mai saurin kisa. Ga kuma yadda ta zuba ayyukan raya kasa. A kan haka ne Samura Kamara, tsohon ministan harkokin waje kuma dan takarart shugaban kasa na jam'iyyar ke cewa:

Jerin gwanon masu kada kuri'uHoto: DW/Abu-Bakarr Jalloh

" Cutar Ebola ta rinka kashe mutane sama da 150 a rana guda. Dalilin ke nan da ya sa wasu jama'a su kai ta "shaci-fadin" kudin da gwamnati ta kashe a lokacin. Zai yi wahala a samu cikakken bayanan nawa aka kashe a wannan lokacin. Ba wai kuma an sace kudin bane ko kuma sun bace. A'a an yi amfani da su ne wurin yakar cutar Ebola. Mun san cewa akwai matsaloli, amma matsalar mu ba ta wuce ta rashin kudi ba. Kuma indai mun samu karin dama za mu fito da wasu hanyoyi da za mu samu karin kudi a aljihun gwamnati domin mun san cewa jamaa na da tsammanin muyi abubuwa sosai a kasar nan."

Jam'iyyu 16 suka tsayar da 'yan takara na neman shugabancin kasar ta Saliyo. Kuma galibinsu na kalubalentar gwamnatin da cewa ta gaza farfado da tattalin arzikin 'yan Saliyo, inda suka ce sakamkon yadda jam'iyyar APC ta lalata tattalin arzikin kasar, kashi 70 cikin dari na mutanen kasar na rayuwa kasa da mizanin talauci.

Amma ita gwamnatin ta hakikance ta yi abin azo-a-gani. Irin wanann dambarwa ce dai ta sa jama'an kasar ke ganin a wanann karon, sai sun duba da kyau kafin su kada kuri'arsu. Desmond Lewis, wani dan kasar ne:

Dangwala yatsa lokacin zabeHoto: DW/A.-B. Jalloh

"Ni dai a ganina siyasa ba za ta iya biya ma mutum bukatun shi ba. Gaskiya ba na jin dadin yadda al'amurra ke gudana a kasar nan tamu."

Zaben dai shi ne karo na biyar tun bayan da Saliyo ta fita daga yakin basasa. Kuma shugaba mai ci Ernest Bai Koroma ya yi mulkin shekaru 10 wato biyar sau biyu. A bisa tsarin mulkin kasar ba zai sake tsayawa takarar shugaban kasa ba. Mutane sama da milyan uku ake saran za su kada kura'a a wannan babban zabe, inda fafatawar za ta fi zafi tsakanin 'yan takara uku Samura Kamara na jam'iyyar APC mai mulki, da tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja Brig Julius Maada Bio na babbar jam'iyyar adawa ta SLPP sai kuma Kandeh Yumkella na jam'iyyar NGC.