1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zaben shugaban kasa: Kamaru ta haramta gamayyar jam'iyyu

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 14, 2024

A cikin watan Disamban bara ne dai jiga-jigan adawar kasar suka kafa wannan gamayya, karkashin jagorancin Jean Michel Nintcheu da kuma Maurice Kamto da ya yi takarar shugabancin kasar a shekarar 2018

Hoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

Yayin da ya rage watanni 18 a gudanar da zaben shugaban kasa a Kamaru, gwamnatin kasar ta ayyana gamayyar hadin kan jam'iyyun siyasar kasar na APC da ATP a matsayin haramtaccen tsari da ya sabawa doka, inda ta gargade su da su gaggauta tarwatsa shirin.

Karin bayani:Jagoran 'yan adawa na Kamaru ya mutu

Ministan harkokin cikin gida na kasar Paul Atanga Nji ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda kamfanin dillancin AFP na Faransa ya rawaito.

Karin bayani:Cece-kucen siyasa ya barke a Kamaru

A cikin watan Disamban bara ne dai jiga-jigan adawar kasar suka kafa wannan gamayya, karkashin jagorancin Jean Michel Nintcheu da kuma Maurice Kamto da ya yi takarar shugabancin kasar a shekarar 2018.