1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasar Masar

May 24, 2012

Al'umar kasar Masar sun fito ka'in da na'in don kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar

epa03231675 An Egyptian man lets his granddaughter casts his ballot paper in the first round of the presidential elections in Cairo, Egypt, 23 May 2012. Egyptian voters, on 23 May, queued at polling stations for the first Presidential election since the ouster of former president Hosni Mubarak in February 2011. The first round vote is on 23 and 24 May. EPA/KHALED ELFIQI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Dubu dubatan Misirawa ne suka yi dafifi a rumfunan zabe, a zaben shugaban kasa tun bayan juyin-juya-halin da ya hambarar da Husny Mubarak.

Tun asubahin fari wasu suka fara yin layi a rumfunan zabe a jihohin 27 da ke fadin kasar Masar don zaben daya daga cikin 'yan takara 13 wasunsu karkashin jam'iyyu, wasu kuma masu zaman kansu. Zaben da kimanin mutane miliyan 50 za su yi ,za kai kwanaki biyu a jere ana gudanar da shi. Rahotanni na nuni da fara gudanar da zaben cikin lumana,in banda harbe wani dan sanda da wasu da ake zatan masu kisan daukar fansa ne suka yi a wata rumfar zabe.

Komai na tafiya cikin tsanaki

Sabannin zabubbukan da aka yi shekarun baya, wadanda 'yan banga da jami'an tsaro ke cin karensu babu babbaka, a wannan karon masu kada kuri,an sun ce sun ga banbanci:

Hoto: Reuters

"Ba wata tursasawa ko razana masu zabe, ko bad da wani abu don a zabi wani, mutane duk sun fita cikin murna da walwala,matasa da dattawa, kowa ya fito don ya zabi wanda yake so"

Wani da ya yii jimirin jira kan layin zabe, duk da tsananin ranar da ake yi ,ya yi bayanin dalilinsa nayin hakan:

"shekaru ishirin ko talatin kenan ina jiran wannan rana. Yau kamar wata ranar sallah ce gare ni don sauke nauyin da ke kaina dangane da kasata da yayana."

Ita ma wannan tsohuwa da ta dogaro ta zo wurin zaben ta bayyana irin fatar da take da ita:

"Na fito ne don zabar dan takarar da ya fi nagarta, don kasarmu ta bunkasa ta fi kowace kasa a duniya"

"Dafifin da ya wuce yadda hukumar zabe ta yi hasashe ,ya sanya hukumar sake tura wasu jami'anta zuwa rumfunan zabe don gyara layuka da kauce wa furmutsitsi. Jami'an tsaro sun tsare wasu wakilan jam'iyu da ke tallata 'yan takararsu a cikin rumfunan zabe.

Za a mika ragamar mulki ga wanda zai yi nasara

Tuni dai kakakin majalisar dokokin kasar Muhammad Katattni ya bayyana aniyar majalisar ta ba wa duk wanda ya lashe zaben cikakken goyan baya don tunkarar matsalolin tsaro da tatttali da suka addabi kasar tun bayan faduwar gwamnatin Mubarak watanni 15 da suka gabata. A nasu gefen, 'yan takarar 12 sun bayyana gamsuwarsu da yadda zaben ke gudana da kuma aniyarsu ta amincewa da sakamakon zaben matukar ya ci gaba da gudana kan gaskiya da rashin rufa-rufa.

Jimmy carterHoto: AP

Su kuwa matasan da suka faro fafutukar juyin juya hali a kasar, wadanda suka ki kafa jam'iya ko tsayar da dan takara sun ce gagarumin aikin da ke gabansu shine sanya ido su ga an aiwatar da sahihancin zabe da kuma tabbatar da cewa shugaban da aka zaba ya aiwatar da manufofin juyin-juya-hali.

Tsohon shugaban Amirka Jimmy Carter da kingiyarsa ta lura da zabe na daya da cikin kungiyoyin kasa da kasa da suka zo kasar don gane wa idonsu yadda zaben ke gudana.

Idan dai har ba a samu dan takara daya da ya yi nasara a zaben ba, to 'yan takara biyu da suka fi samu kuri'a za su je zagaye na biyu-lamarin da ya sa ake zaton samun zaben a wata mai zuwa.

Daga kasa za a iya sauraron sautin wannan rahoto.

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Usman Shehu Usman