1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasar Poland

October 23, 2005

An kammala zagaye na biyu kuma na karshe a zaben shugaban kasar Poland. To sai dai kamar a zagayen farko a wannan karo ma mutane ba su fita sosai wajen kada kuri´a ba. Binciken jin ra´ayin jama´a da aka gudanar ya yi nuni da cewa yin canjaras tsakanin ´yan takara biyu wato Donald Tusk da Lech Kaczynski. Wanda ya yi nasara a zaben dai shi zai gaji shugaba mai barin gado Aleksander Kwasnieswki wanda wa´adin shugabancinsa karo na biyu ya kare.