1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Ana fafata zaben shugaban kasar Peru

Suleiman Babayo LMJ
June 6, 2021

Mutanen kasar Peru na zaben shugaban kasa zagaye na biyu inda ake fafatawa tsakanin Keiko Fujimori 'yar tsohon shugaban kasar Alberto Fujimori da Pedro Castillo sabon shiga a harkokin siyasa.

Peru | Wahlen werden vorbereitet
Hoto: Luka Gonzales/AFP

Ana zaben lokacin da ake ci gaba da fuskantar annobar cutar coronavirus wadda ta halaka fiye da mutane 180,000 a kasar tare da jefa wasu milyoyin mutane cikin kangin talauci.

An yi zagaye na farko na zaben kasar ta Peru da ke yankin kudancin Amirka a watan Afrilu inda 'yan takaran biyu suka fi samun kuri'u kuma wannan zaben zai tantance wanda zai jagoranci kasar na gaba tsakanin Pedro Castillo dan shekaru 51 da haihuwa malamin makaranta da Keiko Fujimori 'yar shekaru 46 da haihuwa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW