Zaben shugabanni a wasu kasashen Afirka
August 3, 2017Talla
Ana sa ran samun sauyi a matakan shugabancin kasashen Senegal da Kenya da kuma Burundi. A kasar Senegal dai kawancen jam'iyyu masu goyon bayan Shugaba Macky Sall ne suka lashe zaben 'yan majalisa da aka yi a kasar. Kasashen Burundi da Kenya kuwa, za su yi zaben shugaban kasa ne a ranakun da ke tafe. Ruwanda za ta yi zabenta ne a ranar Juma'a 4 ga watan Agusta, yayin da ita kuwa da Kenya za ta zabi nata shugaban a ranar Talata 8 ga watan na Agusta.
Masana da 'yan kasa sun yi sharhi kan wadannan zabuka da akasari ake ganin jijiyoyin wuya sun tashi.