1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben 'yan majalisa da kanselolin Kamaru

September 30, 2013

'Yan Kamaru na kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokoki da kuma kanseloli. Jam'iyyar shugaba Paul Biya ake sa ran za ta lashesu saboda rashin hadin kan 'yan adawa.

Hoto: AFP/Getty Images

Ita dai jam'iyyar RDPC ko CPDM da ke rike da madafun ikon Kamaru ta juma tana cin karenta ba tare da babbaka ba a majalisar dokokin kasar. Ko da a zaben shekara ta 2007, sai da ta lashe kujeru 157 daga cikin 180 da majalisar ta kunsa; lamarin da ya bata damar samun rinjaye da take bukata wajen ci-gaba da tafiyar da harkokin mulki. Shi ma dai shugaban kasar Paul Biya mai shekaru 80 a duniya ya sake lashe zaben shugaban kasa a karo na shida a jere a 2011 shekaru 30 bayan hawarsa kan kujerar mulki. Ya cimma wannan buri nasa ne sakamakon rarrabuwar kawuna da ake samu daga bangaren 'yan adawa wadanda suka tsayar da 'yan takara daban daban har guda 22 a zaben.

Ana zargin hukumar zabe ELECAM da zama 'yar amshin gwamnatiHoto: DW

Sai dai kuma Eric Mathias Owona Nguini masani siyasar Kamaru ya ce rashin shunfudu kwakwaran tubalin mulkin demokaradiyya ne ya ke bai wa Paul Biya da jam'iyyarsa damar kai labarai. A cewarsa a wannan karon ma dai matar jiya ba za ta canza zani ba

"Wadannan zabuka ba wani abin da zai dangantasu da na tafarkin demokaradiyya duk da cewa jam'iyyu da dama ne suka shiga don a dama da su. Idan aka yi la'akari da yadda aka tsayar da ranar zabe, da kuma yadda aka kayyade 'yan takara a kowace mazaba, da ma dai rashin nada 'yan baruwanmu a hukumar zabe, za a gane cewar har yanzu babu demokaradiyya a Kamaru."

Rawar ketare a demokaradiyyar Kamaru

Shi dai wannan malamin kimiyar siyasa a jami'ar Yawunde ta biyu ya nemi kasashen yammacin duniya irin su Faransa da Jamus, da su matsa wa shugaba Paul Biya lamba domin ya mutunta shika-shikan mulkin demokaradiyya. Sai dai ya ce sabanin haka, ba sa ce masa ko da ci- kanka sai idan tasu ta hadasu. A lokacin da ya ke mayar da bahasi game da wannan batu Andreas Mehler kwararre a fannin siyasar Afirka a cibiyar nazarin al'amuran kasa da kasa na Leibniz, ya ce abu ne mai matikar wuya saboda Kamaru na daya cikin daidaikun kasashen yankin tsakiyar Afirka da ba a tashin hankali a cikinsu. Saboda haka ne ya ce sai 'yan kasar sun tashi tsaye za su samu taimako daga ketare.

Jam'iyyar Paul Biya na cin karenta ba tare da babbaka baHoto: AP

"Ina ganin cewa daga cikin kasar ne ya dace a samu matsin lambar da za ta tilasta wa gwamnati girka tsarin demokaradiya. Ba abin da kasashen waje za su iya yi illa basu kwarin guywa. Amma dai ina ganin cewa har ya zuwa yanzu ba su dsamu wannan kuzari ba."

Kungiyar Amnesty International ta nunar da cewa Paul Biya na amfani da sandarsa ta mulki wajen tursasa wa duk wadanda suka nuna maitarsu a fili game da harkokin mulki. Yana zarginsu da marar hannu a harkar cin-hanci da karbar rashawa wajen mayar da su saniyar ware, tare da dauresu a gidan yari.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW

Karin labarai daga DW