1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya: Ana zaben 'yan majalisa

April 11, 2019

Kasa ta biyu da ta fi yawan al’uma a duniya Indiya, ta fara zaben ‘yan majalisar dokokinta a ranar Alhamis din nan, inda ra’ayoyi tsakanin masu son Firmanista Narendra Modi da adawa ke kara zafi.

Wahl in Indien 2009
Wasu Indiyawa a lokacin zaben 2009Hoto: Deshakal Chowdhury/AFP/Getty Images)

Zaben na wannan lokacin, Indiyawa miliyan 900 ne aka yi wa rajistar zaben wakilan majalisar dokokin su 543, a zaben da aka fara 11 ga watan Afrilu a mataki na farko. Za kuma a kammala shi ne a ranar 19 ga watan gobe, sannan a kidaya kuri’u a ranar 23 ga watan na gobe. Sama da mutane miliyan 84 ne da suka hada da matasan da ke zabensu na farko su miliyan 15 ke zabe a kashin na farko da ake yi a wannan Alhamis. 

Kwararru na cewa jam’iyyun siyasa a Indiya, za su salwantar da kudade ne galibi a gangamin yakin neman zabe musamman wadanda ake yi ta shafukan sada zumunta na zamani da suka hada da Facebook da Twitter da ma WhatsApp.

An dai zabi Firaminista Narendra Modi ne shekaru biyar da suka gabata tare da alkawuran kyautata tattalin arziki cikin gaggawa da kuma rage matasa marasa ayyukan yi. Akwai dai ci gaba ta fannin hanyoyin mota da kuma na jiragen kasa cikin tsukin da ya yi a mulki, sannan mazauna yankunan karkara na yaba wa kokarin da ya yi wajen sama masu iskar gas na girki da a baya babu ita.

Firaminista Narendra Modi lokacin da ya je hedikwatar jam'iyyar BJPHoto: Ians

Jam’iyyarsa BJP na kuma amfani da rikicin nan da ke tsakanin kasar da Pakistan, wajen janyo hankalin jama’a don ta sami kuri’u a zaben. To sai dai tattalin arzikin kasar ya ja baya kamar yadda bangaren samar da ayyukan yi shi ma ya fuskanci koma bayan da ba a ga irinsa ba sama da shekaru 45 da suka gabata.

Akwai ma zargin da ake yi wa jam’iyyar BJP da goyon bayan kungiyoyin nan na masu kisan wadanda ke cin naman shanu, saboda yadda ake daraja saniyar a Indiya a matsayin abin bauta, sai dai wasu ‘yan jam’iyyar na musanta hakan.

Ko da yake da wuya a iya yin hasashen yadda zaben na Indiya zai kaya, wani gwanin kimiyyar hasashen zabe a Indiya da ake kira Deshmukh ya ce lamarin zai dogara ne da tsarin dabarun da bangaren adawa ta yi nan da ‘yan makonni.

A wani matakin ko-ta-kwana dai, jam’iyyar ta Narendra Modi, ta shirya hada karfi da wasu kananan jam’iyyu ta yadda idan ta gaza kai bantenta da rinjayen da ake bukata kamar yadda ta samu a shekara ta 2014 ba, tana iya kafa gwamnati.