Al'ummar kasar Cote d'Ivoir na zaben 'yan majalisa
December 18, 2016Talla
Wannan zabe na a zaman na farko a karkashin sabuwar jamhuriya ta uku bayan zaben rabagardama da ya amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar a watan Oktoban da ya gabata. A cewar hukumar zaben kasar ta CEI, za a rufe runfunan zaben ne da misalin karfe shida na yamma agogon GMT, sannan kuma sakamakon zaben zai iya kai wa ranar Laraba kafin a same shi, sai dai kuma ana iya samun sakamakon wuccin gadi kafin wannan rana.
Duk da ana cewa mata za su taka rawar gani a fagen siyasar kasar ta Cote d'Ivoir, amma kungiyar mata da ke fafutikar samun daidaito tsakanin maza da mata a kasar, na ganin cewa babu takarar mata da yawa a zaben, inda ta ce mata 43 ne kawai daga cikin 'yan takara 1,337 ke yin takarar.