1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Olaf Scholz ka iya zama shugaban gwamnatin Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe SB
September 26, 2021

Kwarya kwaryar sakamakon zaben Jamus na nuna cewar jam'iyyar SPD ta mataimakin shugaban gwamnati Olaf Scholz, ita ce ke da rinjayen kujeru fiye da CDU ta Angela Merkel.

Bundestagswahl 2021 | Wahlparty der SPD
Hoto: Michael Sohn/AP/picture alliance

 

Sakamakon farko na kuri'un da kada kudi'a ya nunar da cewar babu ratar a zo a gani tsakanin jam'iyyar SPD ta Olaf Scholz da CDU ta masu ra'ayin mazan jiya a zaben 'yan majalisar tarayya da aka gudanar a yammacin wannan Lahadi, wanda kuma ke share fagen kawo karshen mulkin Angela Merkel. Wani binciken jin ra'ayin masu kada kuri'a da gamayyar tashoshin rediyo da talabijin na ARD ta fitar ya nuna cewa jam'iyyar CDU-CSU karkashin jagorancin Amin Laschet ta sami kashi 25% na kuri'un da aka kada, wanda ya yi daidai da kuri'un da Jam'iyyar SPD ta samu . Sai dai lamarein ya sha bamban a sakamakon da tashar talabijin ta ZDF ta fitar inda ta nunar da cewa SPD na kan gaba da kashi 26%, yayin da CDU-CSU ke da kashi 24%.

Hoto: Florian Gaertner/photothek/picture alliance

Tuni ma babban sakataren jam'iyyar SPD Lars Klingbeil ya bayyana cewar dan takararsu ne Jamusawa suka ba wa ikon kafa gwamnati ta gaba, inda ya ce a bayyane yake cewa SPD ta yi nasara, lamarin da zai ba ta damar kafa gwamnati ta gaba. Idan wannan sakamakon ya tabbatar bayan kirga daukacin kuri'u to Olaf Scholz, mataimakin shugaban gwamnati kuma ministan kudi na gwamnatin mai barin gado zai sami damar maye gurbin Angela Merkel, wacce ta shafe shekaru 16 a kan kujerar mulkin Jamus. Ga ma abin da Scholz ke cewa bayan samu nasara:

"Wannan abu ne da ya tabbata cewa 'yan kasa da dama sun kada wa SPD kuri'a, saboda suna son canjin gwamnati, kuma sunan so Olaf Scholz ya zama shugaban gwamnati na gaba."

Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Ko ma ya sakamakon karshe zai kasance dai, Jam'iyyar CDU ta fuskanci koma baya da ba a taba ganin irin sa ba tun 1949, inda ta yi asarar kaso akalla 8% idan aka kwatanta da zaben 'yan majalisar dokoki da ya gudana a 2017. Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 72 da jam'iyyar CDU ta masu ra'ayin mazan jiya ta sami kasa da kashi 30% na kuri'un da aka kada. Wannan ya haifar da rudu a karshen mulkin Angela Merkel, wanda duk da farin jininta ta kasa samar da dan takarar da zai iya maye gurbinta ba. Sai dai har yanzu Amin Laschet na jam'iyyar CDU na da yakinin iya kafa gwamnati idan ya sami goyon bayan wasu jam'iyyu, saboda ya yaba matsayin da jam'iyyarsa ta CDu ta samu.

"Wannan rawa ce ta muka taka rawar gani, kuma za mu iya kokarinmu don yin nasarar kafa gwamnati. Wannan ne burin da na sa a gaba, kuma shi ne burin da muka sa a gaba gaba dayan mu."

Hoto: Wolfgang Rattay/Reuters & Martin Meissner/AP/picture alliance

 Jam'iyyar The Greens wacce ta shiga majalisa ta Buntestag a zabukan baya ta yi nasarar kafa tarihi, inda a karon farko ta sami kashi 10.7% na kuri'un da aka kada, lamarin da ya sa ta zarta da maki shida bajintar da ta nuna a zaben 2017. 'Yar takarar Annalena Baerbock ta yi tsakanci a kan wannan zabe tana mai cewa

"Ba mu sami wannan goyon baya don yi wa 'yan gaba aiki ba, amma mun sami kwarin gwiwa domin mu kawo sauyi. Wannan ne abin da sakamakn wannan zabe ya nuna."

Hoto: Sebastian Gollnow/Pool/REUTERS

Jam'iyyar FDP da ke da sassaucin ra'ayin ce ta zo a matsayi na hudu tare da kusan kashi 10%, kuma ita ce ta zama madogar wajen samar da shugaban gwamnatin Jamus na gaba.

Ita kuwa jam'iyyar AfD mai kyamar baki wacce ta shiga Bundestag a zaben 2017 ta sake samun dama, inda a wannan karo ta sami tsakanin 10 zuwa 11% nan kuri'un da aka kada. Ana ganin cewa rikice -rikicen cikin gida da ta fuskanta ne suka sa ta samun komabayan idan aka kwatanta da zaben da ya wuce inda ta samu 12.6%.

Ko ma dai ya za ta kaya dai, a karon farko na tarihin Jamus za a sami gwamnatin hadaka da ta kunshi akalla jam'iyyun akalla hudu. Za a shafe tsawon lokaci ana tattaunawar share fagen gwamnati a kasar Jamus da ka zama ja gaban nahiyar TUrai a fannin tattalin arziki. Tuni dai Jam'iyyar Green ta riga ta nuna sha'awar hada gwiwa da jam'iyyar SPD wajen kafa gwamnati ta gaba.