Jaridun Jamus: Zaben Yuganda ya dau hankali
January 16, 2026
Jaridar Zeit Online ta rubuta sharhinta mai taken: "Zaben 'yan majalisa da na shugaban kasa cikin yanayi na rashin Intanet: Yoweri Museveni ya shafe shekaru 40 yana kan mulki a Yuganda, kuma da alama zai ci gaba da kasancewa haka". Jaridar ta ce an gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a Yugana, cikin yanayi na danniya.
An bude rumfunan zabe da sassafe, sai dai duk da haka an ga dogayen layuka na mutane a wajen wasu rumfunan zaben, saboda samu jinkirin kai kayayyakin zabe kuma ba a kawo kayan zabe ba, sai bayan lokacin da aka tsara fara kada kuri'a wato karfe bakwai na safe. A lokaci guda kwanaki da dama gabanin zaben, an yi suka sakamakon katsewar Internet da aka bayyana a matsayin wani mataki na danne dimukuradiyya da Shugaba Yoweri Museveni ya dauka. Babu tantama game da nasarar zarcewar Museveni a karo na bakwai, mutumin da ya shafe shekaru 40 yana kan mulki.
Wasu 'yan takara bakwai suna fafatawa da shi, amma ana ganin ba su da damar tabuka komai. Akwai imanin cewar, Museveni na iya tabbatar da ikonsa ta hanyar danne dukkan 'yan takarar adawa. 'Yan adawar, sun yi ta kira ga masu zabe miliyan 21 da suka cancanci kada kuri'a, su shiga zaben na ranar Alhamis duk da barazana da suka fuskanta. Daya daga cikin 'yan takara kuma fitacce da suka fafata har a baya da Museveni shi ne Robert Kyagulanyi, wanda aka fi sani da Bobi Wine. Duk da haka, jami'an tsaro sun sha yin katsalandan a gangamin yakin neman zabensa.
"Somaliya ta karbi shugabancin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya", wannan shi ne taken labarin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta wallafa a dangane da shugabancin karba-karba na zauren da ke birnin New York da aka bai wa gwamnatin da ke Mogadishu, wadda ke fama da talauci, da ta'addanci, da kuma rarrabuwar kawuna. Ana daukar Somaliya a matsayin kasar da ta gaza, a bara kasar ta kasance ta 192 a cikin ma'aunin ci-gaban Majalisar Dinkin Duniya.
Sudan ta Kudu ce kawai ta fi muni, sai dai duk da haka tun a 2025 Somaliya ta kasance daya daga cikin mambobi 10 marasa kujerar din-din-din a kwamitin da ke zama mafi muhimmanci a cikin dukkan hukumomin Majalisar. A ranar daya ga watan Janairun 2026, Somaliyar ta karbi shugabancin Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniyar na wata-wata, inda yanzu take jan akalar manufofin duniya.
A yayin wa'adin shugabancin Somaliya akwai muhimman batutuwa da suka hada da makamai masu guba a Siriya da Dakarun Wanzar da Zaman Lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasashe dabam-dabam, baya ga binciken kotun duniya da ke hukunta manyan laifuka a kan Sudan. Kuma tuni jakadan kasar Abukar Dahir Osman ya ce, Somaliyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen nuna kwarewa da yin adalci d neman hadin kai da cimma yarjejeniya a kan wadannan muhimman batutuwa.
Ita kuwa jaridar Bild online ta yi nata sharhin ne mai taken: "Kara fadada filin jirgin sama mafi girma a Afirka". A cewar jaridar sabon filin jirgin sama da ke kusa da Addis Ababa ba wai kawai zai zama mafi girma a Afirka ba ne, zai ma kasance daya daga cikin manyan cibiyoyin duniya. Cikin alfahari ne dai firaiministan Habasha Abiy Ahmed ya ce aikin zai zama babban wurin samar da kayayyakin more rayuwa na jiragen sama a tarihin Afirka, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito. A cewar kamfanin jirgin sama mallakar gwamnati na Ethiopian Airlines wanda ya ba da kwangilar, filin jirgin saman zai iya daukar jirage 270 da fasinjoji miliyan 110 a kowace shekara, wanda ke nufin ninka karfinta na yanzu sau hudu.