1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Yuganda ya gudana cikin matakan tsaro

Binta Aliyu Zurmi
January 14, 2021

Al'ummar kasar Yuganda sun kada kuri'a da nufin zaben shugaban kasa da 'yan majalisa. Sai dai hukumomi sun jibge jami'an tsaro tare da katse intanet domin gudun tashin hankali.

Afrika Uganda Wahlen Bobi Wine, Popstar und Präsidentschaftskandidat der Opposition
Hoto: Jerome Delay/dpa/AP/picture alliance

An gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu a kasar Yuganda bisa tsattsauran matakin tsaro, inda aka jibge soji da 'yan sanda. Tun kafin wannan ranar dai hukumar kasar ta shaidar da mumunar yakin zabe da ba a taba gani ba a Yuganda, inda da aka samu asarar rayuka musamman a bangaren madugun adawa Robert Kyangulani da aka yi wa lakabi da Bobi Wine.

Rahotanni sun nunar da cewar an katse hanyoyin sadarwa na intanet a kasar, lamarin da ya hana al'ummar kasar ta Yuganda watsa yadda zaben ke gudana a kafofin sadarwar na zamani.


Shugaba Yoweri Museveni na neman wa'adi na 6. Kungiyar tarayyar Afirka kadai ce ta aika da masu sa ido a zaben na Yuganda. Yayin da Amirka da ke zama babbar mai bai wa kasar tallafi, ta sanar da soke aikin sa idon bayan da aka ki ba wa tawagagi izinin sa ido a zaben.