1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Mutanen 104 sun halaka a Brazil

Suleiman Babayo LMJ
February 17, 2022

An tabbatar da samu karin mutanen da ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa suka halaka zuwa 104 a kasar Brazil.

Unwetter in Brasilien
Hoto: Silvia Izquierdo/AP/picture alliance

A kasar Brazil mahukunta sun tabbatar da mutane 104 suka halaka sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa da aka samu a tsaunikan jihar Rio de Janeiro. A wannan Alhamis bangaren aikin 'yan gwana-gwana na jihar ya bayyana alkaluman.

Ruwan sama da ake shakawa cikin wannan wata na Febrairu ya janyo ambaliyar ruwan gami da zabtarewar kasar.

Shugaba Jair Bolsonaro na kasar ta Brazil wanda yanzu haka yake ziyara a kasashen ketere ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta taimakon mutanen da bala'in ya ritsa da su.